Dawisu: Lauyoyi sun bukaci Jami’an DSS su saki Salihu Tanko Yakasai, sa'o'i bayan an cafke shi

Dawisu: Lauyoyi sun bukaci Jami’an DSS su saki Salihu Tanko Yakasai, sa'o'i bayan an cafke shi

- Lauyoyin Alhaji Tanko Yakasai sun rubuta takarda saboda tsare Dawisu

- H.A Gudaji & Co sun bukaci Jami’an DSS su fito da Salihu Tanko Yakasai

- Yau kwana 3 kenan da DSS ta yi ram da tsohon Hadimin gwamnan Kano

Wasu lauyoyi sun rubuta takarda zuwa ga jami’an tsaro na sirri watau DSS a game da tsare Salihu Tanko Yakasai da su ka yi na tsawon kwana da kwanaki.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa wasu Lauyoyi a karkashin H. A Gudaji & Co. sun rubuta takarda zuwa hedikwatar DSS da ke birnin tarayya Abuja.

H. A Gudaji & Co ta aika takarda ne a madadin Alhaji Tanko Yakasai OFR, wanda ya nemi a fito masa da ‘dansa da aka yi ram da shi tun a ranar Juma’a.

Lauyoyin su ka ce sun samu tabbacin cewa jami’an DSS ne su ka kama Malam Salihu Tanko Yakasai, kuma su ka tsare shi har zuwa yanzu bai fito ba.

KU KARANTA: Za ka ɗaukaka a siyasa - Fayose ga Dawisu

Wadannan kwararrun lauyoyi su na ofishi a babban birnin tarayya Abuja, Kano da jihar Jigawa.

Takardar da aka rubuta take cewa: “A matsayinku na hukumar da gwamnati ta kafa bisa tsarin doka, mu na bukatar wadannan abubuwa biyu daga ofishinku.”

  1. A ba mu damar ganin wannan Bawan Allah, Salihu Tanko Yakasai (wanda aka fi sani da Dawisu/Peacock) a matsayinmu na Lauyoyi
  2. Ku saki Salihu Tanko Yakasai (wanda aka fi sani da Dawisu/Peacock) ta hanyar bada beli.

KU KARANTA: Ganduje ya sallami hadiminsa, Salihu Tanko Yakasai

Dawisu: Lauyoyi sun bukaci Jami’an DSS su saki Salihu Tanko Yakasai, sa'o'i bayan an cafke shi
Salihu Tanko Yakasai Hoto: @Dawisu
Asali: Twitter

Wannan takarda da Armaya’u Yusuf Abubakar esq. ya sa wa hannu a madadin H. A Gudaji & Co, ta bukaci DSS su amince da rokon da su ka gabatar a gabansu.

Lauyoyin sun dogara ne da kundin tsarin mulki wajen mika wa jami’an tsaron kokon bararsu.

Yanzu nan labari yake zuwa mana cewa hukumar 'yan sandan farar hula, SSS, ta saki Malam Salihu Tanko Yakasai 'Dawisu' bayan ya yi kwanaki a hannunsu.

Kafin yanzu, Salihu Tanko Yakasai ya na cikin masu magana da yawun gwamnatin Kano.

A lokacin da yake tsare sai aka ji gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganuje, ya bada sanarwar ya tsige hadimin na sa daga aiki saboda sukar gwamnatin APC.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng