Kudin fetur zai iya yin sama yau, Gwamnatin Buhari za ta kai farashin lita sama da N170

Kudin fetur zai iya yin sama yau, Gwamnatin Buhari za ta kai farashin lita sama da N170

- Ana sa ran cewa a yau za a bada sanarwar karin farashin man fetur

- Alamu sun nuna litar mai zai kai N170 zuwa N175 idan aka yi karin

- Hakan na zuwa ne bayan danyan mai ya tashi a kasuwannin Duniya

Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta amince da karin farashin man fetur a makon nan. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa litar man fetur zai iya kai tsakanin N170 zuwa N175 idan aka samu canjin farashi a wannan wata na Maris da aka shiga yau.

Kamfanin NNPC na kasa wanda shi kadai yake shigo da mai a yanzu, ya na kashe N158.33 kafin tacaccen man fetur ya iso Najeriya daga kasashen ketare.

‘Yan kasuwa sun shaida wa jaridar cewa bisa dukkan alamu dole sai farashin litar man ya daga.

KU KARANTA: Ana shirin yi wa Buhari zanga-zanga a kan satar ‘yan makaranta

A makonnin baya, Ministan man fetur, Timipre Sylva, ya bada sanarwar cewa a saurari karin farashi man fetur bayan gangar danyen mai ya kai $60.

Wannan kari da aka samu ya sa ‘yan kasuwa su na kashe N180 kafin kowane lita ya sauka a gidan mai.

Wata majiya daga kamfanin NPMC da ke karkashin NNPC na kasa, ta ce za a sanar da sabon farashin man fetur a yau, Litinin, 1 ga watan Maris, 2021.

“Duk da cewa ‘yan kwadago sun kafe a kan maganarsu na cewa kudin fetur ba zai tashi ba, dole sai an sanar da sabon farashi a wannan makon.” Inji majiyar.

KKU KARANTA: An sa ranar kammala aikin hanyar Legas - Ibadan

Kudin fetur zai iya yin sama yau, Gwamnatin Buhari za ta kai farashin lita sama da N170
Gidan man NNPC
Asali: UGC

Sai dai kuma kamfanin NNPC ta bakin mai magana da yawun ta, Dr. Kennie Obateru, ta bada tabbacin cewa ba za a kara kudin mai cikin kwanakin nan ba.

Tun a watan da ya gabata kun ji cewa 'yan kasuwa sun bayyana cewa a yadda kasuwar Duniya ta ke a yanzu, ya kamata farashin PMS watau man fetur ya tashi.

Muddin gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta shigo da tallafi ba, za a daina saida fetur a N160-N165

‘Yan kasuwa sun hakikance a kan cewa ya kamata litar man fetur ya rika tashi a kan N185 zuwa N200 a gidajen mai. Fetur bai taba kai wannan farashi ba a tarihi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel