PDP ta buƙaci AbdulRasheed Bawa da ya dawo da martabar hukumar EFCC

PDP ta buƙaci AbdulRasheed Bawa da ya dawo da martabar hukumar EFCC

-A kwana-kwanan nan ne dai ka tabbatar da Bawa a matsayin shugaban EFFC.

-Ana kan cigaba da sa ran cewa wannan matashi zai yi rawar gani a hukumar.

-PDP ta shiga sahun masu yi wa shugaban kira wajen kaucewa aikata kuskuren da na baya suka yi.

The Nation ta rawaito cewa, jam'iyyar PDP ta buƙaci Bawa, sabon shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da ya dawo wa da hukumar martabarta.

Jam'iyyar ta shawarci Bawa da ya kaucewa maimaita kuskuren da Ibrahim Magu ya yi ta hanyar gujewa shiga siyasa ko ba da damar amfani da hukumar domin cuzgunawa ko tauye ƴanci ko domin azurta kai kamar "yadda ya faru da shugabanta da ya gabata."

Karanta wannan: Nayi magana da Gwamanoni 5, Minista 1 da aka aukawa mutanenmu a Oyo inji Pantami

EFCC: PDP ta buƙaci Bawa da ya dawo wa da hukumar martabarta
EFCC: PDP ta buƙaci Bawa da ya dawo wa da hukumar martabarta Tushe: Premium Times
Asali: Facebook

A wani jawabi ta bakin kakin Jam'iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan, a rannar Asabar, ya bayyana cewa waɗancan abubuwa su ne suka lalata ƙwarewar hukumar EFFC da kuma jirkita ayyukanta da sa mutane yanke ƙauna da cewa za ta tabbatar da adalci da kuma tafi da ayyuka na yadda ya kamata.

"Muna tuna wa sabon shugaban hukumar EFCC cewa PDP ce ta kafa wannan hukuma ta yaƙi da cin-hanci da rashawa, amma ba a matsayin wata hanya ta cin zali da firgita ƴan Najeriya da ba su ji ba su gani saboda dalilai na siyasa da kuma dalilai na ƙashin-kai."

Karanta wannan: Yadda Shugaban NARICT ya ke tafka barna iri-iri– Kungiya ta rubutawa Gwamnatin Buhari takarda

Sannan ya cigaba da cewa, "PDP ta lura cewa sabon shugaban ya samu horo daga ƙwararru a hukumar wanda hakan ya sa ƴan Najeriya sa ran zai yi amfani da horon da ya samu wajen gyara tsarin aiki da dawo da martabarta daidai da na ƙasashen ƙetare."

"Har'ila yau, Jam'iyyarmu na kira ga shugaban na EFCC cewa, ta la'akari da shekarunsa da horansa, ya kamata ya nuna kyakkyawan misali ga ƴan baya wajen sakawa ƴan Najeriya saboda ƙarfin guiwar da suke da shi a kan sa."

A wani ɓagaren kuma, rundunar ‘yan sanda ta Abuja ta kama mutum arba’in da ake zargi da laifin satar mota, fataucin muggan kwayoyi, fashi da makami da sauran laifuka a yankunan Abaji, Gwarinpa, Asokoro, Jabi-Daki biyu da Mabushi.

An kama wadanda ake zargin a yayin kai samame da sintiri tsakanin ranakun 18 zuwa 24 ga Fabrairu, 2021, Vanguard News ta ruwaito.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar ta Abuja, ASP Yusuf Mariam ya lissafa wadanda ake zargin kamar haka: Tijani Zariwa dan shekara 25, Shamsudeen Abdullahi dan shekara 20, Muktari Mohammed dan shekara 48, Yahaya Abdullahi dan shekara20, Abbas Mohammed dan shekara 24.

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel