An gano dajin da yan bindiga suka ajiye yan matan makarantar Jangebe

An gano dajin da yan bindiga suka ajiye yan matan makarantar Jangebe

- Yan bindiga a Zamfara sun shiga daji da dalibai mata sama da 300 da suka sace

- Iyaye yara da dama sun shiga cikin daji ceton yaransu

- Wannan shine karo na biyar da za'a sace daliban makaranta a arewacin Najeriya

An ga dalibai mata sama da 300 da aka sace daga makarantar sakandaren GGSS Jangebe, karamar hukumar Talata Mafara, a dajin Dangulbi.

Wani malamin makaranta wanda yayi magana da Daily trust ranar Asabar kuma ya bukaci a sakaye sunansa ya ce daga cikin dalibai 600 dake makarantar, 50 kadai suka rage.

Amma hukumar yan sandan jihar ta ce dalibai 317 aka sace, yayinda kwamishanan labaran jihar, Alhaji Sulaiman Tunau Anka, ya ce su basu san adadin daliban da aka sace ba.

A daren jiya ne aka tattaro cewa jami'an tsaro da jami'an gwamnatin Zamfara sun gano wadanda suka sace yaran.

"Ana rike da yaran a dajin Dangulbi, karamar hukumar Maru," wata majiya ta bayyana.

Dazukan dake Dangulbi sun shahara da kasancewa mabuyar yan bindiga na tsawon shekaru.

DUBA NAN: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna

An gano dajin da yan bindiga suka ajiye yan matan makarantar Jangebe
An gano dajin da yan bindiga suka ajiye yan matan makarantar Jangebe
Asali: Getty Images

DUBA NAN: Janathan ya samu lambar yabo ta Zaman lafiya na Afirka na shekarar 2020

A bangare guda, cikin yunkurin nasaran ceto dalibai mata 317 da aka sace ranar Juma'a, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya nemi taimakon tubabbun dan bindiga Auwalu Daudawa da Zakoa Buhari.

Auwalu Daudawa ne dan bindigan da ya jagoranci satan daliban makarantan sakandaren GCSS, Kankara, a jihar Katsina.

Zakoa Buhari kuma shine dan shahrarren kasurgumin dan bindiga, Buhari Daji.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel