Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Zamfara ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwana a jihar

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Zamfara ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwana a jihar

- Gwamnan Zamfara ya yi jawabinsa na farko tun lokacin da aka sace dalibai a Jangebe

- Matawalle ya jaddada niyyarsa na cigaba da sulhu da yan bindiga

- Wannan shine karo na farko da za'a sace dalibai a jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara, Muhammad Matawalle, ta bada umurnin rufe dukkan makarantun kwana dake jihar gaba daya, rahoton TVC.

Matawalle ya yi hakan sakamakon sace daliban makarantar sakandaren GGSS Jangebe da aka sace a karamar hukumar Talata Mafara dake jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a a Gusau, birnin jihar.

Matawalle ya jaddada cewa zai cigaba da shirin yin afuwa ga yan bindiga domin su ajiye makamansu.

A cewarsa, harsashi ko da guda daya ne a hannun dan bindiga na da hadari ga al'ummar jihar.

"Yanzu haka, an tura jirage masu saukar angulu na yan sanda domin ceton yaran. Za'a sanar da iyayen yara da jama'a halin da ake ciki game da wannan yunkuri da ake yi," Matawalle yace.

"Yayinda muke kokarin karfafa tsaro a makarantun mu, na bada umurnin kulle dukkan makarantun sakandare na kwana dake fadin jihar."

DUBA NAN: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Zamfara ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwana a jihar
Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Zamfara ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwana a jihar Credit: Channels TV
Asali: UGC

DUBA NAN: Baku fi ƙarfin gwamnati na ba, Buhari ya gargaɗi ƴan bindiga

Mun kawo muku rahoton cewa ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata 317 daga makarantar sakandiren GSS Jengebe, karamar hukumar Talata Mafara dake jihar Zamfara.

Majiyoyin sunce an sace wadannan dalibai ne misalin karfe daya na dare.

Wasu yan asalin garin biyu sun bayyana cewa anyi awon gaba da kannensu mata.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel