Gwamnatina za ta agaza wa matasa miliyan ɗaya a kowacce shekara

Gwamnatina za ta agaza wa matasa miliyan ɗaya a kowacce shekara

-Ƴan takara na yin alƙawura masu yawa a lokacin neman zaɓe sai dai cika su ne kan kasance abu mai wahala.

-Sai ga shi wani ɗan takara na kuma tsohon gwamnan babban bakin Najeriya na wani gagarumin alƙawari.

-Ya tabbatar da cewa idan aka zaɓe shi zai samar da abubuwan yi ga matasa.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa wani tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ne, Prof. Chukwuma Soludo, ya tabbatar da cewa in dai aka zaɓe shi a matsayin gwamna a zaɓe mai zuwa na 6 ga watan Nuwamba, to zai agaza wa matasa miliyan ɗaya a kowanne wata.

Farfesa Saludo dai yana takarar gwamnan ne a jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), kuma ya yi wannan kalami ne a Awka ta jihar Anambara.

Solude, farfesan Fannin Sanin Tattalin Arziƙi, ya nuna cewa nasarar jam'iyyar a zaɓe mai zuwa shi ne manuni na makomarta a matsayin jam'iyyar siyasa.

KARANTA WANNAN: Gwamnan Oyo ya amince da hutun sabon shekarar musulunci a jiharsa.

Gwamnatina za ta agaza wa matasa miliyan ɗaya a kowacce shekara
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Soludo. Source: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

Ya buƙaci APGA da su yi bakin ƙoƙarinsu wajen amfani da hanyoyi da za su ba wa jam'iyyar nasara.

A cewarsa, "manufata shi ne aiki da dukkan mambobi na wannan jam'iyya a ko'inna suke a ƙasar nan. Zan canja APGA daga jam'iyyar siyasa zuwa jam'iyya ta haɗin kai."

KARANTA WANNAN: Gwamnan Ondo ya sha alwashin dawo da gwamna Obaseki apc bayan watanni 8 kacal a PDP

Sannan ya ƙara da cewa, "tsararren burin Anambara na 2070 abu ne da za a cimma nan da shekara hamsin kuma ni zan tabbatar da faruwar hakan domin inganta rayuwar ƴaƴanmu da za su zo a nan gaba."

"Sannan, wannan zaɓe na da muhimmancin gaske kuma bai kamata wani ya yi wasa da hakan ba. APGA kusan shekaru sha biyar kennan tana bunƙasa jihar. Duk da kuwa ƙarancin samun kuɗi daga asusun gwamnatin tarayya, jihar na ta ƙoƙari na ganin ta ƙarasa babban filin tashi-da-saukan jiragen sama da Ɗakin Taro da Filin wasan ƙwallon ƙafa."

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu rahoton wasu zargin manyan sata 25 da aka tafka, wanda su ka jawo wa gwamnati asarar Naira biliyan 900.

Kungiyar Human and Environmental Development Agenda (HEDA) ta aika wasika zuwa ga Muhammadu Buhari a makon nan.

Kungiyar HEDA ta yi gargadi cewa ana awon-gaba da kudin al’umma, wanda hakan ya sa ake wasa da yaki da rashin gaskiyar da gwamnatin nan ta ke yi.

Sunana Anas Dansalma kuma na karanta harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Ni marubuci ne kuma mafassari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel