Gwamnan Ondo ya sha alwashin dawo da Gwamna Obaseki APC bayan watanni 8 kacal a PDP
- Gwamna Rotimi Akeredolu ya ce zai dawo da Gwamnan Edo zuwa APC
- Gwamna Godwin Obaseki ya bar APC ya koma PDP ne saboda ya zarce
- Akeredolu ya ce sai ya yi bakin kokarinsa wajen raba Gwamnan da PDP
Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, ya ce takwaransa na Edo, Godwin Obaseki, zai dawo jam’iyyar APC mai mulki da ya bari a shekarar bara.
Godwin Obaseki ya sauya-sheka daga APC ya koma PDP ne bayan an hana shi takara da sunan cewa akwai alamun tambaya game da wasu takardunsa.
A karshe Gwamnan ya doke Osagie Ize-Iyamu, ya lashe zaben jihar Edo a jam’iyyar PDP mai adawa.
Da yake magana a lokacin da aka sake rantsar da shi a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya ce Obaseki ya dawo APC.
KU KARANTA: Gwamnati za ta dakatar da yawo da Makiyaya su ke yi da dabbobi a Ogun
“Sun ce ka dawo tafiyar APC, kuma mu na murna da ka dawo mana.” Inji Rotimi Akeredolu, yayin gode wa manyan da su ka halarci bikin rantsar da shi.
Gwamnan Edo ya yi maza ya nuna alama da jikinsa da ke nuna sam-sam, bai sauya-sheka daga PDP ba.
Daily Trust ta ce daga nan sai Mai girma gwamna Akeredolu ya ce: “Idan har su ba za su iya dawo da kai (zuwa jam’iyyar APC ba), to ni zan dawo da kai.”
Jaridar ta ce ragowar gwamnonin da aka yi wannan a gabansu sun hada da Gboyega Oyetola, Babajide Sanwo-Olu, Dapo Abiodun da Kayode Fayemi.
KU KARANTA: Gwamnan Oyo ya amince da hutun ranar sabuwar shekarar musulunci
Asiwaju Bola Tinubu da tsohon shugaban APC, Bisi Akande sun halarci taron, inda aka rantsar da gwamnan tare da Lucky Aiyedatiwa, a matsayin mataimakinsa.
Majalisar dattawan Najeriya ta fito ta kare kanta a kan tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC da ta yi a ranar Larabar nan.
Kamar Yadda Sanata Suleiman Abdu Kwari ya yi bayani, Bawa ya kare kansa a gaban majalisar tarayya, kuma Sanatocin kasar sun gamsu da bayanan da ya yi masu.
Abdulrasheed Bawa wanda ya yi shekara 16 a EFCC shi ne 'dan-cikin gida da ya fara rike hukumar.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng