Yanzu-yanzu: Ɓata-gari sun kai wa 'yan sanda hari, sun kashe biyu, sun cinnawa motarsu wuta
An kashe yan sanda biyu a Ekwulobia, hedkwatar karamar hukumar Aguta da ke jihar Anambra. Daily Trust ta ruwaito.
A halin yanzu ba a game samun cikakken bayani kan abinda ya wakana ba amma an ce maharan sun yi awon gaba da makaman jami'an yan sandan.
Hakan na zuwa ne kwana guda bayan an kona wani ofisishin yan sanda a garin Aba, jihar Abia.
'Yan sanda biyu ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon mummunan lamarin.
DUBA WANNAN: Hotunan auren mace mai shekaru 91 da mijinta mai shekaru 71 da aka daura bayan shekaru 10 suna soyayya
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kashe 18, sun kone gidaje sun sace shanu a Kaduna
Tunda farko, yayin taron manema labarai a ranar Laraba, Frank Mba, kakakin rundunar yan sanda ya ce an kashe wasu daga cikin wadanda ake zargi da kai hari a Aba an kuma kama wasu.
Ya bayyana sunan wadanda suka rasu kamar haka; ASP Vincent Gonze da Saja Emmanuel Okoronkwo.
Ya ce, "Wasu bata gari da adadinsu ya kai 200 dauke da bindigu AK-47 da adduna sun kai hari ofishin yan sanda sun kone wurin da fetur da wasu abubuwa masu fashewa.
"Sakamakon harin, jami'an yan sanda biyu, ASP Vincent Gonze da Saja Emmanuel Okoronkwo sun riga mu gidan gaskiya."
A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.
Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng