‘Yan bindiga sun kashe mutane 3, sun yi gaba da Amarya da mata 8 a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane 3, sun yi gaba da Amarya da mata 8 a Katsina

- ‘Yan bindiga sun shiga garin Sabuwa a makon nan, sun sake yin ta’adi

- Rahotanni sun ce an kashe wasu maza uku, sannan an yi gaba da mata

- Daga cikin matan da aka dauke, har da wata da ta yi aure kwanan nan

Akalla mutane uku su ka mutu a sakamakon harin da wasu da ake zargin miyagun ‘yan bindiga ne, su ka kai karamar hukumar Sabuwa, jihar Katsina.

Rahoto daga jaridar Vanguard ya bayyana mana cewa wadannan ‘yan bindiga sun kuma yi gaba da wasu mata da kananan ‘yan mata akalla tara a yankin.

Wannan lamari ya auku ne ranar Talata, 23 ga watan Fubrairu, 2021, a wasu kauyuka uku: Mai Bakko, Kawarawa, da Unguwar Bako da ke garin Sabuwa.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka 'Yan bindiga a Zamfara

Majiyar jaridar ta tabbatar cewa an kai wa mutanen karamar hukumar Sabuwa wannan hari ne cikin dare.

Wadanda su ke zaune a wadannan kauyuka sun bada sunayen wadanda aka kashe da: Ahmed, Jabir, da Abubakar. Babu wani karin bayani a kan shekarunsu.

Wata majiyar ta kuma bayyana cewa akwai wata da ba ta dade da yin aure ba a cikin matan da aka yi garkuwa da su, amma ba mu da karin haske a kan batun.

‘Yan sandan jihar Katsina ba su yi magana a game da wannan hari ba, amma ba wannan ne karon farko da ‘yan bindiga su ka kai irin wannan hari a Sabuwa ba.

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya ya jawo za a kawo dokar haramta kiwo a fili a Ogun

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu su ke kiran a zauna ayi sulhu da wadannan miyagun ‘yan bindiga. Wasu a gefe guda, su na ganin bai dace ayi hakan ba.

A makon nan mu ka ji wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu kan da'awar Sheikh Ahmad Gumi na shiga daji, ya na yi wa 'yan bindiga wa'azi su daina ta'adi.

Wasu sun nemi gwamnati ta gaggauta kama malamin tare da yi masa tambayoyi kan yadda aka yi ya san mafakar 'yan bindigan da su ke hallaka Bayin Allah a kasar.

Wasu su na ganin malamin yana da kyakkyawar masaniya dangane da inda 'yan bindigan su ke.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng