Za a haramtawa Makiyaya yawo da dabbobi su na kiwo a Jihar Ogun inji Majalisa

Za a haramtawa Makiyaya yawo da dabbobi su na kiwo a Jihar Ogun inji Majalisa

- Ana shirin kafa dokar da za ta kawo karshen kiwo da dabbobi a fili a Ogun

- Majalisar dokoki ta ce hakan zai yi maganin rikicin makiyaya da manoma

- An kafa irin wannan dokar a Benuwai inda aka haramta gantalin dabbobi

Shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Rt. Hon. Olakunle Oluomo, ya ce akwai shiri da ake yi a majalisar na kawo dokar da za ta haramta kiwo a fili.

Olakunle Oluomo ya bayyana cewa za ayi doka a kan kiwo da sauran harkokin da su ka shafi dabbobi domin maganin rikicin makiyaya da manoma.

Jaridar Punch ta rahoto shugaban majalisar ya na wannan bayani a lokacin da ya gana da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu a Abeokuta.

An yi wannan gana wa ne tare da su Yinka Folarin a harabar majalisar da ke Oke-Mosan, Abeokuta

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: Wasu Fulani sun roki al’umma gafara a Oyo

Hon. Olakunle Oluomo ya ce sun zauna da wasu jagororin Arewa, wadanda su ka soki yadda dabbobi su ke gantali, su na yawo da sunan kiwo a kasar.

Wannan lamari ya jawo rigima tsakanin makiyaya da manoman jihar musamman a yankin Yewa.

Oluomo yake cewa majalisa ta kammala shirin zama da masu ruwa da tsaki domin jin ta bakinsu, wajen kirkiro hukumar da za ta kula da alkaluman jama'a.

Wannan hukuma da za a kirkiro za ta dauki nauyin tattara alkaluman mutanen da ake da su a Ogun, sannan za ta rika kula da su saboda a inganta tsaro.

Za a haramtawa Makiyaya yawo da dabbobi su na kiwo a Jihar Ogun inji Majalisa
Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

KU KARANTA: Majalisar Dattawa za ta tattauna a kan rikicin makiyaya da manoma

Da yake kero irin kokarin da wannan majalisar tayi, Oluomo, ya bayyana yadda su ka amince da dokar da ta yi sanadiyyar kafa jami’an tsaro na Amotekuun.

A jiya ne mu ka ji cewa kungiyar Gwamnoni ta na la’akari da yiwuwar a zauna a sasanta da ‘Yan bindiga ayi sulhu domin ayi maganin matsalar rashin tsaro.

Hakan na zuwa ne bayan wasu Gwamnoni sun ziyarci Neja bayan an sace mutane da dama.

Gwamnan na Ekiti yake cewa za su yi duk abin da ta kama domin ganin wannan rikici ya zama tarihi. “Sai mun duba abubuwan da su ka fara sababba rikicin.”

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel