Adadin wadanda suka mutu a harin Maiduguri ya tashi zuwa 16

Adadin wadanda suka mutu a harin Maiduguri ya tashi zuwa 16

- Yan ta'addan Boko Haram sun kai mumunan hari birnin Maiduguri

- Gwamnan Borno ya tabbatar da cewa harin ya shafi akalla mutum 60

- Sama da mutane 10 sun mutu yayinda kimanin 50 sun jigata

Adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai Maiduguri, birnin jihar Borno ya tashi zuwa 16, jami'an asibiti sun bayyana.

Da farko, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, bayan ziyarar da ya kai asibitin koyarwan jami'ar Maiduguri da babban asibitin jihar, yace mutane 10 suka mutu kuma 47 sun jigata.

Amma sabbin bayanai daga majiyoyi daga asibitocin biyu sun tabbatar da cewa adadin ya tashi daga 10 zuwa 16, ThisDay ta ruwaito.

Daya daga cikin majiyoyin, ma'akaciyar jinya, ta ce mutum uku suka mutu a daren Talatan da gwamnan ya je.

Tace: "An ce mutane shiga suka mutu daga asibitocin biyu bayan 10 da aka kawo a mace."

"Uku sun mutu kafin wayewar gari kuma sauran ukun sun mutu da safen nan. Muna addu'a kada wasu su kara mutuwa saboda akwai wadanda ke cikin halin ha'ula'i."

KU KARANTA: 'Yan bindiga daga saman bishiya sun sheke dan sanda, sun raunata wasu 3 a Neja

Adadin wadanda suka mutu a harin Maiduguri ya tashi zuwa 16
Adadin wadanda suka mutu a harin Maiduguri ya tashi zuwa 16 Hoto: Governor of Borno State
Source: Facebook

DUBA NAN: Abin da yasa muka tuba muka miƙa makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ziyarci asibitoci biyu ranar Laraba, bayan harin da yan ta'addan Boko Haram suka kai Maiduguri inda suka kashe mutane 10 kuma 47 suka jigata.

A jawabin mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau ya saki, Gwamnan ya bayyana cewa yan ta'addan sun harba roka unguwannin Gwange, Adam Kolo.

Ya ce a unguwar Gwange rokan ya fi hallaka mutane inda ya sauka wajen wasan yara.

Zulum yace: "Lallai abin takaici ne ga mutan Borno da gwamnatin jihar, kimanin mutane 60 abin ya shafa, 10 sun mutu."

"Ya faru sakamakon harbin da yan ta'addan sukayi ne. Mun fuskanci irin haka shekara daya da ya wuce."

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel