Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da AbdulRasheed Bawa matsayin shugaban EFCC

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da AbdulRasheed Bawa matsayin shugaban EFCC

Majalisar dattawan Najerita ta amince da AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.

Shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan, ya sanar da hakan a zauren majalisan ranar Laraba, 24 ga Febrairu, 2021.

Wannan ya biyo bayan tambayoyi da ya amsa yayinda ya gurfana gaban yan majalisan.

Mun kawo muku cewa majalisar dattijai ta fara tantance sabon Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sanata Babajide Omoworare ne ya gabatar da Bawa wanda tuni ya kasance a dakin taron.

Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da AbdulRasheed Bawa matsayin shugaban EFCC
Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da AbdulRasheed Bawa matsayin shugaban EFCC Credit: @NGRSenate
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel