Dan baiwa: Dan shekara 16 ya kera murhu mai amfani da batir

Dan baiwa: Dan shekara 16 ya kera murhu mai amfani da batir

Wani yaro dan shekara 16 da haihuwa ya kera murhun girki mai amfani da wutar lantarki da batiri da kuma kuma gawayi

Dan baiwa: Dan shekara 16 ya kera murhu mai amfani da batir
Ndyson na nunawa jama jama'a murhun nasa mai amfani da batir

Wani yaro dan shekara 16 da haihuwa ya kera wani murhun girki mai ban al'ajabi da ke mai amfani da wutar lantarki, da batiri, da kuma kuma gawayi.

Yaron dan asali garin Onisha dan dan baiwa, mai suna Ndyson ya zo garin Aba ne da wannnan murhu mai ban mamaki da al'ajabi wanda ya kirkira da kansa, ya kuma ke sarrfawa shi din nunuwa jama'a, ya kuma sa masa sunan 'murhun Ndyson'.

Wata mai amfani da dandalin sada zumunta na Facebook mai suna Ugochinyere ce, ta lika hotunan yaron, da kuma murhin nasa mai ban mamaki bayan ta gan shi a garin Aba gwadawa jama'a yadda ya ke aiki.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka samu masu basirar kirkira irin wannan a Najeriya ba, a kwanan baya ma wani ya saka hotunan wani yaro mai kimanin shekara 7 ya kera motocin wasan yara daga arewacin kasar.

Ko a karshen shekarar 2016 da ta wuce, wasu 'yan Najeriya sun kera motar sulke ta zamani sun kuma mika ta kyauta ga rundunar sojin kasar a matsyin gudunmawa .

Aiko da naku ra'ayin dangane da wannan labari zuwa http://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a http://www.twitter.com/naicomhausa

Ga hira da wasu 'yan Najeriya kan farsashin kayyaki a kasuwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng