Babbar magana: Sanatan Kogi ya kira Gwamnan Jihar Abia da ‘Dan-giya’ a tsakar Majalisa

Babbar magana: Sanatan Kogi ya kira Gwamnan Jihar Abia da ‘Dan-giya’ a tsakar Majalisa

- Sanata Smart Adeyemi ya kira Gwamna Okezie Ikpeazu da Mashayin giya

- Adeyemi ya yi hakan ne da nufin ya kare Gwamnan jihar Kogi daga suka

- Ana rade-radi ne Sanatan Abia, Enyinnaya Abaribe, ya soki Yahaya Bello

Jaridar Daily Trust ta ce an kai ruwa-rana a majalisar dattawa bayan Sanata Smart Adeyemi (APC, Kogi) ya bayyana gwamnan jihar Abia da ‘dan-giya.

Sanatan jihar Kogi ta yamma, Smart Adeyemi, ya jefi Gwamna Okezie Ikpeazu, da cewa ya na shan giyar ‘Champagne’, a lokacin da ake zaman majalisa.

‘Dan majalisar ya na maida martani ne ga abokin aikinsa, Enyinnaya Abaribe, wanda ya fito daga Abia.

Smart Adeyemi ya furta wannan magane ne domin ya kare gwamnan jiharsa ta Kogi, Yahaya Bello, wanda ake jita-jitar Enyinnaya Abaribe ya caccake shi.

KU KARANTA: Ortom: Muddin aka ga baya na, alhakin rai na ya na wajen Gwamna Bala

Sanata Adeyemi ya ke cewa yayin da wasu gwamnoni su ka damu da walwala da kare hakkin talakawansu, mutanen jihar Abia su na hannun ‘dan-giya ne.

“Ko da wasu gwamnoni, na kokarinsu, mu (mutanen Kogi), mun yi sa’a, mun yi dace da mu ka samu gwamnan da ya ba sha’anin tsaro muhimmancin gaske.”

“Mun yi iyaka da jihohi tara.” Amma Kogi ba ta fuskantar matsalar tsaro inji Sanata Adeyemi.

“A wasu jihohin da muke da tarin masu ilmi, masu basira, da kokarin neman kudi, irin Abia da ‘yan giya ke mulkinsu. Gwamnan Abia Mashayin‘ Champagne’ ne."

KU KARANTA: Akwai yiwuwar fetur ya tashi, Gwamnati ta ce ba ta da kudin biyan tallafi

Babbar magana: Sanatan Kogi ya kira Gwamnan Jihar Abia da ‘Dan-giya’ a tsakar Majalisa
Sanata Smart Adeyemi Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

Da abin ya kai haka, sai Ahmad Lawan ya ja-kunnen Adeyemi, ya bukaci ya nemi afuwa. Abaribe ya ce karya ake yi masa da aka ce ya soki gwamnan na Kogi.

A kokarin kare gwamnan Kogi ne Sanatan na APC ya soki gwamnan Abia. Sanata Abaribe ya yi tir da martanin da Adeyemi ya yi, ya na mai dogara da jita-jita.

Yanzu nan mu ka ji jam'iyyar Peoples Democratic Party watau PDP ta saka baki a rikicin da ake yi tsakanin gwamna Samuel Ortom da gwamnaBala Mohammed.

Jam'iyyar ta yi kira ga gwamnonin na ta biyu su yi hakuri da junansu, su maida wukakensu, bayan Samuel Ortom ya kai ga kiran takwaran na sa 'dan ta'adda.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel