Buhari da Gwamnoni za su yi zaman musamman a makon nan game da farashin fetur inji Minista

Buhari da Gwamnoni za su yi zaman musamman a makon nan game da farashin fetur inji Minista

- Chris Ngige ya yi zaman karshe da wakilan kungiyoyin kwadago a jiya

- Ministan ya ce ya rage wa Shugaban kasa ya gana da gwamnonin jihohi

- Za ayi zama domin a duba sha’anin farashin man fetur a ranar Alhamis

Ministan kwadago, Chris Ngige ya ce shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai hadu da gwamnonin jihohi inda za su tattauna a kan farashin fetur.

Jaridar Punch ta rahoto Ministan kwadago da aikin yi, Sanata Chris Ngige ya na cewa za ayi wannan zama ne a ranarAlhamis, 25 ga watan Fubrairu, 2021.

Chris Ngige ya yi wannan bayani ne a ranar Lahadi, bayan ya jagoranci gwamnatin tarayya yi zaman karshe da kungiyoyin kwadago a fadar Aso Villa.

Ministan ya ce sun duba aikin da kwamitin da aka kafa domin duba farashin man fetur ya yi, kuma ma’aikatarsa ta gabatar da bukatu zuwa ga hukumar NNPC.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya na shirin yin ƙarin kuɗin dakon mai

Ya ce: “Bangaren kwadago sun lura cewa sun ce wani abu, kuma kamar yadda na fada, ana cigaba da aiki a kan batun. Gwamnoni za su zauna a ranar Alhamis.”

An yi wannan magana a taron majalisar tattalin arziki, saboda haka kowa ya san halin da ake ciki. Mun samu kanmu a cikin matsi, babu kudin biyan tallafi.

“NNPC sun yi bayani; su na shigo da kaya ne. Idan gwamnati ta zare hannunta, farashi ya danganta ne da yadda kaya su ka zo.” Ministan ya yi karin-bayani.

Sanata Ngige ya ce amma akwai yiwuwar NNPC su samu rangwame wajen shigo da man fetur.

KU KARANTA: Alkali ta ce a tsaida aikin jawo gas batan mutanen gari sun je kotu

Buhari da Gwamnoni za su yi zaman musamman a makon nan game da farashin fetur inji Minista
Wasu Gwamnoni a taro a Aso Villa
Source: Facebook

Kuma su na amfani da kudin kasar waje da aka saida masu ne da rahusa. Ba a kasuwa su ke sayen dala ba. Saboda haka za a duba duk wadannan idan an zauna.

Ministan harkokin mai na Najeriya ya ce ana ta aikin hako mai a Arewa. Timipre Sylva ya bayyana kokarin da ake yi na samar da mai da ya yi magana kwanaki.

Sylva ya koka da cewa annobar COVID-19 ya kawo ja-baya wajen harkar mai da gas a Duniya.

Minista tarayyar ya kuma yi magana game da satar danyen mai da fasa bututu da ake yi, ya ce an samu raguwar wadannan laifuffuka a gwamnatin Muhammadu Buhari.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel