Manyan 'yan bindiga uku sun sake tuba sun mika makamansu a Zamfara

Manyan 'yan bindiga uku sun sake tuba sun mika makamansu a Zamfara

- Manyan yan bindiga uku sun tuba sun mika makamai sun rungumi zaman lafiya a jihar Zamfara

- Yan bindigan sun mika makamansu ne a ranar Litinin a gidan gwamnati da ke Gusau inda suka rantse da Al-Kurani ba zasu sake komawa laifi ba

- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya yi farin ciki kan nasarar da ake samu a kokarin samar da zaman lafiya a jihar

Wasu hatsabiban yan bindiga uku sun sake tuba sun mika makamansu ga gwamnatin jihar Zamfara, Channels Television ta ruwaito.

Bayan mika bindigunsu kirar AK-47 da wasu makamai a ranar Litinin, yan bindigan sunyi rantsuwa da Al-Kur'ani mai tsarki cewa ba za su sake komawa yin fashi ba.

KU KARANTA: Yin sulhu da 'yan bindiga yana da hatsari, in ji HURIWA

Manyan 'yan bindiga uku sun sake tuba sun mika makamansu a Zamfara
Manyan 'yan bindiga uku sun sake tuba sun mika makamansu a Zamfara. Hoto: Channels Television
Asali: Twitter

Daya daga cikinsu da ya yi magana cikin harshen Hausa a gidan gwamnatin da ke Gusau ya ce sun amshi tsarin afuwa da gwamnatin ta fitar kuma ba za su sake komawa aikata munanan ayyuka ba.

A bangarensa, Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta karbe bindigu daga hannun yan bindigan.

DUBA WANNAN: Nan ba da daɗewa ba Boko Haram za su iya haɗewa da ƴan bindiga, Sheikh Gumi

Gwamnan ya ce hakan ya zama dole domin samar da zaman lafiya da bawa yan jihar dama su yi aikinsu lafiya kalau.

Ya yi amanna cewa wasu daga cikin fulani dama bata gari ne, ya ce wasu daga cikinsu dole ce tasa suka fara aikata laifuka.

"Muna gode wa Allah da yasa muka sake ganin irin wannan nasarar. Da muka fara sulhu da wannan mutanen, wasu na ta sukar mu saboda ba su fahimci lamarin ba," in ji gwamnan.

Ya ce wasu na magana ne kan rashin tsaro ba tare da sanin abinda ya haifar da shi ba.

A bangarensa, kwamishinan yan sandan jihar, Abutu Yaro, ya yabawa gwamnatin jihar saboda shirin samar da zaman lafiyar inda ya ce ana samun nasara.

Ya kuma yi kira ga yan bindigan su mika makamansu su tuba domin a samu zaman lafiya a jihar.

A farkon watan Fabrairu, 8 daga cikin yan bindigan sun tuba sun mika makamansu ga gwamnatin jihar ta Zamfara.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164