2023: Jiga-jigan siyasan Yarbawa sun dura Ogun, sun fara nemawa Tinubu goyon-baya
- Kungiyar South West Agenda 23 ta dage da yi wa Bola Tinubu fafutuka
- SWAGA23 ta ce babu wanda ya dace ya mulki Najeriya irin Bola Tinubu
- Shugaban SWAGA 23, Dayo Adeyeye, ya kai yakin zabensu zuwa Ogun
Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso yamma sun shiga jihar Ogun domin nema wa Bola Tinubu goyon-baya a zaben 2023.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa shugabannin jam’iyyar ta APC sun dura Ogun ne a karshen makon nan, domin fara yi wa Bola Tinubu yaki.
Tsohon Ministan ayyuka kuma shugaban kungiyar South West Agenda 23, Dayo Adeyeye, ya jagoranci tawaga zuwa fadar Sarkin Remoland, Babatunde Ajayi.
Sanata Dayo Adeyeye ya bukaci Mai martaba Babatunde Ajayi ya sa masu albarka a fafutukar da su ke yi na ganin Bola Tinubu ya samu tikitin takara a 2023.
KU KARANTA: Labari mai zafi: Gwamnan Imo ya damke Sanata Okorocha
Bayan nan, ‘yan kungiyar ta kungiyar South West Agenda 23 sun kai wa tsohon gwamnan Ogun, Gbenga Daniel, ziyara a gidansa da ke Asoludero, garin Sagamu.
Da yake jawabi a wajen da su ka kai ziyara, Adeyeye ya bayyana cewa tsohon gwamnan Legas, Tinubu ne ya fi kowane mutumin Kudu cancantar ya nemi takara.
Sanata Adeyeye ya ce: “Tinubu zai yi kasuwa, bai bukatar a tallata shi, kuma ya bada gudumuwa sosai wajen cigaban kasar nan. ‘Dan siyasa ne mai son cigaba.”
“Mu na da shiyyoyi uku a Kudu, dukkansu su na da damar takara. Kudu maso yamma ta na neman kujerar shugaban kasa, wanda zai taimaka mana shi ne Tinubu.”
KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya iya bakinsa - inji Gwamnan Ondo
Tsohon Ministan ya ce idan su ka dage, hakarsu za ta cinma ruwa, ya ce kungiyar SWAGA 23 ta shiga Oyo da Osun, kuma za a bude rasosshi a Kogi da Akwa Ibom.
Kwanakin kun ji wani jagoran jam'iyya mai mulki ta APC, Tujnde Balogun, ya bayyana yadda aka kulla wata yarjejeniya tsakanin Muhammadu Buhari da Bola Tinubu.
Tunde Balogun, wanda shine shugaban rikon jam'iyyar a jihar Legas, ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar Yarabawa za su karbi mulki a 2023 a tafiyar jam'iyyar APC.
Amma wasu masu fashin siyasa su na ganin Bola Tinubu zai iya fuskantar wasu kalubale.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng