‘Yan ta’addan Boko Haram sun yi ta’adi a Borno, sun yanka ‘Yan gudun hijira 5
- Wasu mutane takwas da ke sansanin gudun hijira a garin Dambao sun bace
- Jami’an tsaro na sa-kai sun gano gawar wasu daga cikin wadannan mutane
- An iske gawawwakinsu an yi masu yankan rago lokacin da su ke je faskare
Akalla mutanen da ke gudun hijira biyar ake zargin cewa ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun yanka a karamar hukumar Damboa, jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ‘yan ta’addan sun yanka wadannan Bayin Allah da su ke gudun hijira ne yayin da su ka fita neman itace.
Rahoton ya bayyana cewa wannan lamari ya auku ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Fubrairu, 2021.
Wani jami’in sa-kai mai suna Abu Damboa, ya ce akwai mutane da ke sansanin ‘yan gudun hijira da-dama da yanzu sun bace, ba a san inda su ke ba.
KU KARANTA: Sojoji sun hallaka yan ta'addan Boko Haram a Borno
Malam Abu Damboa ya shaida wa manema labarai cewa shi da sauran abokan aikinsa su na bi gida-gida domin gano wadannan mutane da su ka bace.
“Mun samu rahoto wasu ‘yan gudun hijira sun bace. Saboda haka, mu ka shiga nemansa, amma daga baya mu ka gano an yanka biyar daga cikinsu.”
Abu Damboa ya ce sun tsinci gawar mutanen nan ne kilomita kusan biyu daga inda su ke yankan itace.
Jami’in tsaron na sa-kai yake cewa: “Abu ne mai ratsa zuciya da mu ka ga an yanka Bil Adama kamar wasu dabbobi, duk an jefar da gawawwakinsu.”
KU KARANTA: Boko Haram sun kashe sojoji 9 a Nasarawa
Wata majiyar ta ce: “An gano gawar mutane biyar daga cikin takwas da ake nema.” Tuni dai aka yi masu sutura, aka bizne su kamar yadda addini ya tanada.
A baya kun ji yadda arangama tsakanin Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da mayakan ISWAP ya kawo ajalin mayakan ISWAP masu tarin yawa.
HumAngle ta ruwaito cewa rikici ya barke tsakanin mayakan Boko Haram da 'yan ISWAP a garin Sunawa, jihar Borno, da ke tsakanin iyakar Nijar da Najeriya.
Sojojin Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad wadanda aka fi sani da Boko Haram sun hallaka mayakan ISWAP a dalilin sabanin da ya shiga tsakaninsu.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng