Atiku ya manta da adawar siyasa, ya yabi Buhari a kan shirin yin gwanjon matatun mai

Atiku ya manta da adawar siyasa, ya yabi Buhari a kan shirin yin gwanjon matatun mai

- Atiku Abubakar ya ce ya ji dadi da ya ga za a saida wasu kadarorin Najeriya

- Atiku ya ce da ya yi irin wannan magana a baya, sai Gwamnati ta yi masa ca!

- Tun ba yau ba Atiku yake bada shawarar Gwamnati ta yi gwanjon matatunta

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya na goyon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na wasu daga cikin kadarorin da ta mallaka.

Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne a wani dogon bayani da ya yi a shafinsa na Twitter a jiya.

A jawabin da Atiku Abubakar ya yi wa take da: ‘Privatisation of Refineries and Other Assets: Better Late Than Never’, ya ba gwamnatin kasar shawarwari.

‘Dan siyasar adawar ya bukaci a bi keke-da-keke wajen saida kadarorin kasar, ya ce gara ace an makara, a kan ace ba a yi gwanjon wadannan kadarorin ba.

KU KARANTA: Gwamnati na shirin cin bashin N158b da aka manta da su a bankuna

Jagoran hamayyan ya ce: “Da na ke shugabantar kwamitin saida kadarorin kasa, na kawo wadannan tsare-tsare, wadanda su ka sa tattalin arziki ya motsa da 6%.”

Bayan haka, Atiku ya kara da cewa: “Kuma aka nema wa talakawan mu aikin yi da-dama, dukiyar da aka samu ta sa mu ka rabu da bashi, mu ka samu ‘yanci.”

“Duk da cewa gwamnatin APC ta yi kaca-kaca da shawarwarina a shekarun nan, amma ina mai matukat murna da na ga an ga hikimar yin haka yanzu.” Inji shi.

‘Dan siyasar ya ce yanzu gwamnatin Muhammadu Buhari ta duba ta gano cewa saida matatun mai da wasu kadarorin kasar shi ne zai ceci tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: A inganta mana tsaro, a cire mana takunkumi - Atiku ga Biden

Atiku da Buhari a 2015
Atiku da Buhari a 2015 Hoto: @atiku
Asali: Twitter

“Ba son kai na ke yi ba tun can, burina shi ne in ga an samu zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaban Najeriya. Na yi murna da na ga an dauki wadannan dabaru.”

Mun kawo maku rahoto cewa wasu daga cikin kadarorin da za a saida sun hada da babban dakin taro na ICC, filin Tafawa Belewa, da wasu kamfanonin wutar lantarki.

Idan an yi gwanjon wadannan kadarori, ana sa ran gwamnatin tarayya za ta samu har kusan Naira biliyan 500, wanda za a yi amfani da su a kasafin kudin kasa.

Wasu masana tattalin arziki su na ganin babu bukatar gwamnati ta cigaba da rike wadannan matatu da kadarori wanda ba su jawo komai sai asara duk shekara.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel