Kotu ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tsaida aikin jawo gas daga Ajaokuta a Kano

Kotu ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tsaida aikin jawo gas daga Ajaokuta a Kano

- Wasu Mutanen karamar hukumar Dawakin Kudu sun kai Gwamnati Kotu

- Mazauna yankin Magami sun ce an karbe masu filayensu wajen aikin AKK

- Alkali ta saurari kararsu, ta bukaci a dakatar da wannan aiki a jihar Kano

Babban kotun tarayya da ke zama a Kano, ta yi na’am da rokon da aka kawo mata na dakatar da aikin AKK na jawo karfin gas daga Ajaokuta-Kaduna-Kano.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa Alkali ya amince da karar da wani Abdullahi Adamu da wasu mutane 35 su ka kawo masa a kan wannan aikin da aka fara.

Masu wannan kara sun maka gwamnatin tarayya, Ministan fetur, kamfanin mai na NNPC, ORA da kamfanin Egbunike & Associate a gaban kotun na Kano.

Jaridar ta ce Adamu da kuma sauran mutanen sun nemi a daina wannan aiki a filin da ya ratsa ta kauyen Magami, karamar hukumar Dawakin Kudu, jihar Kano.

KU KARANTA: An kai tsohuwar Ministar Tarayya, Oduah, kotu

Alkali mai shari’a Sa’adatu Mark, ta fara karbar kukan wadannan jama’a, ta bukaci duka wadanda aka yi kara, su dakatar da wannan aiki har sai an karkare zama.

Sa’adatu Mark ta ba wadanda ake tuhuma watau gwamnatin tarayya, Ministan man Najeriya, NNPC da kamfanin da ke wannan aiki wa’adin tsawon mako guda.

A karshen zaman da aka yi, Alkalin ta dakatar da shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Afrilun, 2021.

Lauyan da ya tsaya wa wadannan mutane, Abubakar Ibrahim-Ishaq, ya yi karin haske, ya ce karbe filayen jama’a da aka yi ya saba wa doka, domin ba a bi ka’ida ba.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta yi bikin cika shekara 50, Fadar Shugaban kasa ba ta ce uffan ba

Kotu ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta tsaida aikin jawo gasa daga Ajaokuta a Kano
AKK Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar Lauyan, doka ta bukaci a rubuta takarda a duba darajar filayen al’umma kafin a karbe masu dukiya, ya ce a wajen wannan aiki, ba ayi la’akari da wannan ba.

Dazu kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya manta da adawar siyasa, ya yabi Muhammadu Buhari a kan shirin yin gwanjon matatun fetur.

Atiku Abubakar ya yi tarayya da gwamnatin tarayya wajen saida matatun mai da kadarorin kasa.

Atiku ya ba Buhari shawarar yadda za a bi a saida dukiyoyin da Gwamnati ta mallaka, ya ce ya ji dadi da shugaba Buhari ya ga hikimar da ya dade ya na magana a kan ta.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel