Sojoji sun hallaka yan ta'addan Boko Haram, sun kona motocinsu 7

Sojoji sun hallaka yan ta'addan Boko Haram, sun kona motocinsu 7

- Bayan rahotanni kan harin da aka kaiwa Sojoji Marte, hedkwatar tsaro ta saki jawabi

- DHQ ta bayyana cewa tan samu nasarar kawar da yan ta'addan da suka kai hari

- "Sojojin sama da na kasa suka hada hannu wajen samun nasara kan yan ta'addan"

Hukumar Sojin Najeriya ta alanta samun nasara kan yan ta'addan Boko Haram (ISWAP) da suka yi kokarin kaiwa Sojoji hari a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.

Diraktan yada labaran hedkwatar tsaro, Bernard Onyeko, ya bayyana cewa Sojoji sun samu nasarar hallaka adadin yan ta'addan mai yawa.

Ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Bernard Onyeko yace "rundunar Operation TURA TA KAI BANGO tare da hadin kan mayakan saman Operation LAFIYA DOLE sun ragargaza motocin yakin Boko Haram/ISWAP tare da kashe adadi mai yawa cikinsu yayinda sukayi kokarin kai hari insa suke a Marte."

Ya ce sojojin sun yiwa yan ta'addan kwantan bauna "inda suka bude musu wuta kuma aka samu nasarar nan"

Kalli hotunan:

KU KARANTA: Jami'an Sojoji sun ragargaji yan bindiga a garin Birnin Gwari a jihar Kaduna

Sojoji sun hallaka yan ta'addan Boko Haram, sun kona motocinsu 7
Sojoji sun hallaka yan ta'addan Boko Haram, sun kona motocinsu 7 Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

KU DUBA: Zaben kananan hukumomin Kano: Zamu lashe dukkan kujeru 44, Ganduje ya bayyana

Kun ji cewa yan ta'addan ISWAP sun kai hari, da yammacin Juma'a, barikin Sojoji dake Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Rahoton ya nuna cewa har da safiyar Asabar suna cikin barikin.

Wannan hari na zuwa ne lokacin da gwamnatin jihar Borno ke shirin mayar da mutane 300 garin. A Oktoban 2020, gwamnan jihar ya kaddamar da kwamitoci biyu domin mayar da yan sansanin yan gudun Hijra Marte, Kirawa da Ngoshe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng