Aisha: Buhari ya taya mutum 6 murnar zagayowar ranar haihuwarsu, ya yi banza da Mai dakinsa

Aisha: Buhari ya taya mutum 6 murnar zagayowar ranar haihuwarsu, ya yi banza da Mai dakinsa

- Aisha Buhari ta cika shekara 50, sai kuma aka ji fadar Shugaban kasa ta yi gum

- Shugaban Najeriya bai taya mai dakin ta sa murnar zagayowar wannan rana ba

- A watan nan, Buhari ya taya wasu manyan mutane da suka kara shekara murna

Punch ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya mutane akalla shida murnar zagayowar ranar haihuwarsu a cikin wannan wata na Fubrairu.

Sai dai abin mamaki, a ranar da uwargida Aisha Muhammadu Buhari ta ke bikin kara shekara a Duniya, fadar shugaban kasa ba ta ce mata komai ba.

A ranar farko a watan nan, shugaban kasa ya aika sako, ya na taya macen da ta fara zama Edita a Najeriya, Dr. Doyin Abiola, murnar cika shekaru 75.

Mai girma Muhammadu Buhari ya aika irin wannan sako yayin da Jacob Olupona ya cika shekara 70.

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya yabi Aisha Buhari yayin da ta cika shekaru 50

Kwanaki uku bayan nan, sai Olusoji Akinrinade ya cika shekara 70, a nan ma shugaban kasar ya taya tsohon ‘dan jaridar murnar zagayowar wannan rana.

Sauran wadanda fadar shugaban kasa ta tuna a ranar haihuwarsu a wannan wata sun hada da tsohon mukaddashin gwamnan Taraba, Sanata Sani Danladi.

Haka zalika a ranakun 16 da 19 ga watan Fubrairu, Buhari bai manta da Janar Jeremiah Useni da Sanata Anyim Pius Anyim ba, duk da su na jam’iyyar adawa.

A makon nan da ya gabata ne Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta cika shekaru 50 a Duniya.

KU KARANTA: Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta yi kira a tsare al'umma

Aisha: Buhari ya taya mutum 6 murnar zagayowar ranar haihuwarsu, ya yi banza da Mai dakinsa
Hajiya Aisha Buhari Hoto: www.fmic.gov.ng
Asali: UGC

A ranar 17 ga wata da mai dakinsa, Aisha Buhari ta ke murnar cika shekara 50, babu wani jawabi da ya fito daga shugaban kasar ko hadiman shugaban Najeriyar.

A shekarun baya, wasu daga cikin mukarraban shugaba Muhammadu Buhari su kan aika sako a shafukansu na sada zumunta, su na yi wa Aisha Buhari barka.

Rahotanni sun bayyana cewa tun a karshen shekarar da ta gabata rabon da a ga uwargidar shugaban kasar a Najeriya, lokacin da aka yi bikin auren 'diyarta.

Mutane su na cigaba da cigiya da tambaya ko ina mai dakin shugaban kasar ta su ta shige.

-

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel