Al-Mundahana: Tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama ta gurfana gaban alkali a Abuja

Al-Mundahana: Tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama ta gurfana gaban alkali a Abuja

- Tsohuwar ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah ta gurfana gaban kotun taryya da ke Abuja kan zargin almundahanar kudade

- Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohuwar ministan da wasu mutane takwas da ake zarginsu da hada baki wurin wawurar kudaden al’umma

- Lauyan EFCC, Liman Hassan ya shaidawa kotu cewa hukumar ba ta samu damar mika sammaci ga wasu daga cikin wadanda ake zargin ba don haka ya nemi a bashi lokaci

Tsohuwar ministan sufurin jiragen sama, Stella Oduah a ranar Litinin ta gurfana a gaban kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja kan zargin almubazzaranci da kudade, Channels Television ta ruwaito.

Hukumar Yaki da Masu Ta'annati da Kudade, EFCC, na zargin cewa Oduah ta yi almubarzanci da kudaden gwamnati a lokacin da ta ke aiki a matsayin minista.

DUBA WANNAN: Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa

An gurfanar da tsohuwar minista Stella Oduah a gaban kotu
An gurfanar da tsohuwar minista Stella Oduah a gaban kotu. Hoto: Channels Television
Source: UGC

A cikin karar da suka shigar kan ministan da wasu mutum takwas, EFCC na zarginsu da damfara da karkatar da kudade ta hanyar amfani da asusun bankuna da ba a san wadanda suka mallake su ba.

A farkon zaman, mai shigar da karar, Liman Hassan ya shaidawa kotu cewa hukumar ba ta samu ikon mika takardar gayyata zuwa kotu ga wadanda ake zargi na biyar da shida ba.

DUBA WANNAN: Bayan budurwarsa ta haifa ma sa ɗa, sai ya gudu ya bar gari tare da surukuwarsa

Mai shigar da karar ya roki kotu ta bashi dama ya mika sammacin ga wadanda ake zargin da ya ce kamfanoni ne masu zaman kansu.

Alkalin, Mai shari'a Inyang Ekwo ya tsayar da ranar 19 ga watan Afrilun 2021 domin gurfanar da wadanda ake zargin.

Tunda farko, Inyang Ekwo ya tsayar da ranar 22 ga watan Fabrairu domin gurfanar da tsohuwar ministan da har yanzu ba a mika mata sammaci ba a lokacin da aka ambaci shari'ar a ranar 9 ga watan Fabrairun 2021.

A halin yanzu Sanata Oduah ita ce ke wakiltar mazabar Anambra ta Arewa a majalisar tarayyar Nigeria.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel