Gwamnan Legas ya yabi Uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari yayin da ta cika shekaru 50

Gwamnan Legas ya yabi Uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari yayin da ta cika shekaru 50

- Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya taya Aisha Buhari murnar cika shekara 50

- A yau ne matar Shugaban Najeriyar ta ke bikin ranar zagayowar haihuwarta

- Mista Babajide Sanwo-Olu ya yabi Aisha Buhari, ya kira ta jajirtaciyyar mata

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya taya mai dakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, murnar cika shekaru 50 da haihuwa.

Punch ta ce Mista Babajide Sanwo-Olu ya mika sakon taya murnarsa ne a jiya ranar 16 ga watan Fubrairu, 211, ta bakin babban sakataren yada labarai, Gboyega Akosile.

A jawabin da Mista Gboyega Akosile ya fitar, gwamnan ya bayyana uwargidar Najeriyar a matsayin “jajirtattar mata, mai faram-faram, sannan kuma mai tausayi.”

Gwamnan na Legas ya bayyana Aisha Buhari a matsayin bangon da ta dafa wa shugaban kasar.

KU KARANTA: Hadimin Aisha Buhari ya ki bayyana inda Uwargidan shugaban kasa ta shiga

“A madadin mutanen jihar Legas da kyakkayawar mai dakina, Ibijoke, ina taya ki murna, uwargida, Aisha Buhari, a wannan lokaci da ki ke bikin cika shekaru 50.”

Ya ce: “A ce uwargidarmu ta cika shekaru 50 cikin falalar ubangiji da lafiya, abin ayi murna ne. A shekarun nan, kin nuna sha’awarki wajen taimakon marasa karfi a kasarmu.”

A matsayinki na mai kare hakkin kananan yara da mata, ki na cikin masu sukar yin auren wuri.

Jawabin ya ce: “Sha’awarki ga yara da mata ta sa ki ka kafa kungiyar ‘Future Assured’, domin cigaba da wayar da kai a kan game da lafiya da aikin mata da kananan yara.”

KU KARANTA: Aisha Buhari ta bukaci a kawo karshen matsalar tsaro

Gwamnan Legas ya yabi Uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari yayin da ta cika shekaru 50
Gwamnan Legas, Jide Sanwo Olu Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Gwamna Sanwo-Olu ya ce Aisha Buhari ta dage a kan sai mata sun samu ilmin firamare da sakandare kafin su yi aure. A karshe ya yi mata addu’ar lafiya da tsawon rai.

A watan da ya wuce kun ji cewa Mai dakin shugaban kasar, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ba ta zaune a cikin fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Rahotani sun nuna cewa Aisha Muhammadu Buhari ta na kasar waje tun shekarar bara.

Tun lokacin da Hajiya Aisha Buhari ta fice zuwa birnin Dubai a kasar Tarayyar Larabawa, UAE, ba tare da an ji labari ba, har yau ba ta dawo ba, hakan ya jawo ake ta 'yan surutai.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel