Gwamna Bala na Bauchi ya kiyaye bakinsa, kada ya haddasa rikici a Najeriya: Gwamnan Ondo

Gwamna Bala na Bauchi ya kiyaye bakinsa, kada ya haddasa rikici a Najeriya: Gwamnan Ondo

- Ana cigaba da musayar kalamai tsakanin gwamnan Ondo da na Bauchi

- Da farko Gwamnan Bauchi ya soki gwamnan Benue amma gwamnan Ondo ya tofa albarkacin bakinsa

- Gwamnonin sun samu rashin fahimta ne kan lamarin makiyaya

Gwamnan jihar Ondo, ya siffanta kalaman gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, cewa yan Najeriya basu bukatar izininsa domin shiga dazukan jihar a matsayin "abin ban haushi kuma na rashin tunani."

Akeredolu ya yi kira ga Gwamna Bala ya bi a hankali kada tayar da tarzoma da kalamansa, Vanguard ta ruwaito.

Zaku tuna cewa Akeredolu ya umurci makiyaya su fita daga cikin dazukan jihar Ondo ko kuma suyi rijista.

Gwamnan Ondo ya bayyana hakan ne sakamakon yawaitan garkuwa da mutane, kashe-kashe, fyade, da nau'ikan laifukan daban-daban.

Amma Bala Mohammed yace Akeredolu bai da hakkin hana mutane shiga daji a Najeriya.

Bala yace: "Fili na hannun gwamnatocin jiha da na tarayya amma yan Najeriya basu bukatar izinin gwamnoni ko gwamnatin tarayya kafin su zauna a wani waje."

Martani kan hakan ta bakin hadiminsa na sabbin kafafen yada labarai, Olabode Richard Olatunde, gwamna Akeredolu ya yi kira ga yan Najeriya kada su saurari gwamna Bala Mohammed.

"Ba zan biyewa mutum mai zuciyan rikici ko rigima ba. Duk da cewa kalamansa na da ban haushi kuma suna kunshe da rashin tunani, kawai shawara zamu baiwa gwamna Bala Mohammed kada ya bankawa Najeriya wuta da kalamansa dake da hadari da ka iya raba kan yan kasa," yace.

DUBA NAN: Kada ku daina garkuwa da mutane ku shiga Izalah saboda ta fi muni, Dahiru Bauchi

Gwamna Bala na Bauchi ya kiyaye bakinsa, kada ya haddasa rikici a Najeriya: Gwamnan Ondo
Gwamna Bala na Bauchi ya kiyaye bakinsa, kada ya haddasa rikici a Najeriya: Gwamnan Ondo Credit: Presidency
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya zauna da Dogo Gide, shugaban yan bindiga a dajin Tagina, jihar Neja

A bangare guda, a ranar Alhamis, har an fara sa ran sako dalibai da malaman makarantar GSC Kagara da aka sace, amma aka samu cikas saboda yan bindigan sun tsaya kan bakansu cewa sai an biya kudin fansa N500 million.

Sun bukaci wannan kudi ne matsayin kudin fansan matafiyan motar NSTA da suka sace, da kuma mutane 42 na makarantar GSC Kagara, Thisday ta ruwaito.

Yan bindigan sun kai hari makarantar ne ranar Laraba, inda suka kashe dalibi daya.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel