An maka Gwamnatin Buhari a kotu a kan neman taba tsohuwar ajiyar mutane a bankuna

An maka Gwamnatin Buhari a kotu a kan neman taba tsohuwar ajiyar mutane a bankuna

- Gwamnatin Tarayya za ta karbi aron kudin da aka manta da su a bankuna

- Kungiyar Palm Wealth Shareholders ta garzaya kotu a dalilin wannan shiri

- Shugaban PWSA ya ce mutane za su sha wahala kafin su dawo da kudinsu

Wasu ba su ji dadin kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi na aron kudi Naira biliyan 158 da mutane su ka manta da su a asusun bankuna a Najeriya ba.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa wasu masu ruwa da tsaki, sun kai karar gwamnati a wani babban kotun tarayya da ke zama a Abeokuta, jihar Ogun.

Wadannan mutane sun bukaci a dakatar da gwamnatin tarayya, a hana ta cigaba da shirin da ta ke yi na karbar makudan kudin mutane da aka ajiye a bankuna.

Masu ruwa da tsakin su ka ce zai yi wa wadanda su ka ajiye wannan kudi wahalar iya dawo da kayansu a lokacin da su ka bukata saboda matakan da aka sa.

KU KARANTA: Jihohi sun kai karar Gwamnatin Tarayya a kan dokar E.O 0010

A cewar shugaban kungiyar Palm Wealth Shareholders watau PWSA, Mista Emokeraro Simon, matakan da za a bi wajen karbo kudin su na matukar tsauri.

Wannan ya sa Emokeraro Simon ya roki Alkali ya hana gwamnati dabbaka wannan matakin.

Lauyan Simon ya na ikirarin cewa wannan tsari da aka kawo na cewa idan mutum na bukatar kudinsa, sai ya rubuta takarda, ya ci karo da kundin tsarin mulki.

Wani masanin harkar gwamnati, Joe Abbah, da yake magana a kan canjin da aka yi wa tsare-tsaren tattalin arzikin kasa, ya ce ya na goyon bayan wannan tsarin.

An maka Gwamnatin Buhari a kotu a kan neman taba tsohuwar ajiyar mutane a bankuna
Muhammadu Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: An maka Buhari, Makinde a kotu

Dr. Joe Abbah wanda ya rike shugaban yi wa tsare-tsaren gwamnatin tarayya garambawul a baya, ya ce babu matsala idan an ari kudin da aka ajiye haka kurum.

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike , ya sha alwashin sa kafar wando daya da Gwamnoni 35 da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan zarar kudi daga asusun ECA.

Nyesom Wike ya ce ba ya tare da kungiyar NGF, bai yarda gwamnatin tarayya ta taba asusun ECA ba.

Idan za ku tuna, gwamnan ya ce idan ba za a ba jihar Ribas kason 13%, lallai zai garzaya kotu, kalubalanci matakin cire kudi da za ayi da sunan yaki da matsalar tsaro.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng