Gwamnoni sun ce a dauki rarar kudi ayi maganin tsaro, Gwamna Wike ya ce bai yarda ba

Gwamnoni sun ce a dauki rarar kudi ayi maganin tsaro, Gwamna Wike ya ce bai yarda ba

- Nyesom Wike zai kalubalanci matakin cire kudi da za ayi daga asusun ECA

- Gwamnan ya ce idan ba za a ba jihar Ribas kason 13%, lallai zai garzaya kotu

- Wike ya tambayi inda aka kai $1bn da Gwamnatin tarayya ta dauka a 2017

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi zama da Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a kan matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya.

Jaridar The Nation ta ce a wannan zama da aka yi, Gwamna Nyesom Wike, ya shaida wa Sarkin na Kano cewa bai goyon bayan a taba kudi daga asusun ECA.

Kungiyar Gwamnoni ta NGF ta hadu a kan cewa a cire kudi daga asusun rarar mai na ECA domin gwamnatin tarayya ta iya yin maganin rashin tsaro a kasar nan.

Gwamnan ya yi jawabi ta bakin wani hadiminsa, Kelvin Ebiri, ya ke fada wa Alhaji Aminu Ado Bayero cewa shi da kungiyar gwamnonin sun sha ban-ban ta nan.

KU KARANTA: Yadda mu ka tsira a harin da ‘Yan bindiga su ka kawo - Yaran Kagara

Nyesom Wike yake cewa zai goyin bayan wannan magana ne idan dai za a ba jihar Ribas kasonta na 13% daga cikin wannan kudi da aka tara daga cinikin mai.

Wike ya na mai mamakin inda aka kai Dala biliyan 1 da gwamnati ta dauka daga wannan asusu na ECA a shekaar 2017, ta ce za ta yi maganin ‘Yan Boko Haram.

“Jiya aka fada mani cewa gwamnoni sun yarda za a dauki kudi daga asusun rarar mai, a talllafa wa sojoji. Ina kudin da su ka dauka a baya, $1bn su ka ba sojoji?”

“Yanzu ga wannan, zan fada wa babban lauyan gwamnatina; ‘dole ka shirya, za mu tafi kotu. Ba zan goyi bayan wannan ba, sai dai idan za a ba mu 13% dinmu.”

Gwamnoni sun ce a dauki rarar kudi ayi maganin tsaro, Gwamna Wike ya ce bai yarda ba
Gwamna Nyesom Wike Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Mun gane yadda Ma’aikatu ke awon gaba da kudin Gwamnati – ICPC

A jawabinsa, Wike ya tuna wa Sarki Bayero yadda mahaifinsa ya yi kokari wajen kawo zaman lafiya a fadin kasar nan, ya ce shugabannin zamanin yau, sun saki layi.

Tsohon Shugaban kasa Abdussalami Abubakar ya gargadi Gwamnoni a kan sakin bakunansu. Abdussalami ya ce dole a guji abin da zai sa a sake yin yakin basasa.

Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya ce dole mutanen Najeriya su rungumi zaman lafiya da soyayya domin a guji abin da ya faru tsakanin shekarar 1967 da 1970.

Abubakar ya ke cewa masu shekaru da yawa, sun san abin da ya auku a lokacin da aka yi yakin.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng