Kuma dai! Yan bindiga sun sake kaiwa mutane hari jihar Neja

Kuma dai! Yan bindiga sun sake kaiwa mutane hari jihar Neja

- Kuma dai! wasu yan bindiga sun kai hari jihar Neja, arewa maso tsakiyar Najeriya

- Jihar yanzu na fuskantar matsala da yan bindiga kuma da alamun sun gagari jami'an tsaro

- Yanzu haka, wasu yan bindiga na tattaunawa da gwamnatin jihar don sakin daliban GSC Kagara

Yan bindiga da yammacin Asabar sun sake kai wani sabon hari gundumar Gurmama dake karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

The Nation ta ruwaito cewa da yiwuwan akalla mutane 15 sun nutse cikin ruwa yayinda suke kokarin gujewa yan bindigan.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan sun dira garin da muggan makamai suna harbin kan mai uwa da wabi.

A cewar majiyar da aka sakaye sunansa, mutanen sun gudu cikin rafi don gujewa yan bindigan amma da yawa cikin sun nutse.

"Yanzu haka basu san adadin wadanda suka nutse ba, muna kyautata zaton har yanzu yan bindigan na nan. Ba zamu iya kayyade adadin wadanda suka mutu ba yanzu," yace.

Yunkurin da akayi na ji daga bakin kakakin hukumar yan sandan jihar, Abiodun Wasiu, ya ci tura.

DUBA NAN: Sheikh Gumi ya rokawa 'yan bindiga gafara daga gwamnatin tarayya

Kuma dai! Yan bindiga sun sake kaiwa mutane hari jihar Neja
Kuma dai! Yan bindiga sun sake kaiwa mutane hari jihar Neja
Asali: Original

DUBA NAN: Ina so na iya Turanci sosai, ‘yar shekara 50 da ta shiga JSS2 ta magantu

A bangare guda, a ranar Alhamis, har an fara sa ran sako dalibai da malaman makarantar GSC Kagara da aka sace, amma aka samu cikas saboda yan bindigan sun tsaya kan bakansu cewa sai an biya kudin fansa N500 million.

Sun bukaci wannan kudi ne matsayin kudin fansan matafiyan motar NSTA da suka sace, da kuma mutane 42 na makarantar GSC Kagara, Thisday ta ruwaito.

Yan bindigan sun kai hari makarantar ne ranar Laraba, inda suka kashe dalibi daya.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel