Ku daina garkuwa da mutane amma kada ku shiga Izalah saboda ta fi satar mutane muni, Sheikh Dahiru Bauchi
- Sheikh Dahiru Bauchi ya yi kira ga Fulani su daina aikin fasadi a doron kasa da suke yi
- Ya ce kashe-kashen mutane da sace-sacen mutane ba abu mai kyau bane
- Amma Shehi yace idan suka fita kada su shiga Izalah saboda ta fi muni
Babban Malamin addini kuma jagoran darikar Tijjaniya ya yi kira ga Fulani masu garkuwa da mutane da suyi hattara kada su shiga Izalah bayan fita da laifin satar mutane.
A cewar Malamin, shiga Izalah ta fi aikata laifin garkuwa da mutane hadari da kuma rashin kyau.
A wani faifain jawabi da ya bayyana kafafen ra'ayi da sada zumunta, an ji Sheikh Dahiru Bauchi yana cewa garkuwa da mutane laifi ne, amma Izalah kafirci ne.
Shehi ya kara da cewa Fulani suyi hattara kada su sake shiga wani abu wanda yafi sata da mutane hadari.
"Ina jawo hankali musamman ga Fulani kar kuma su sake shiga wani abu wanda yake kusa da kidnapping. Ina ji musu tsoro kada ku shiga Izalah kuma. Kada su daina fashi da makami kuma su zama yan izalah," Shehi yace.
"Kar ku yadda ku shiga Izalah, kar ku cigaba da satar mutane. Kar ku yadda wadanda su sace muku shanu su dawo su bata ku, su bata muku tunani, su koya muku kashe mutane."
"Ina nanatawa, kada ku fito daga cikin wadannan abubuwan ku fada Izalah saboda idan kuka yi hakan kun fada cikin abinda yafi wannan muni. Da kuna cikin tabo, kun koma kun fada cikin kashi kenan."
KU KARANTA: Mutane a jihar Borno sun gudu daga muhallansu yayinda Soji suke artabu da Boko Haram
DUBA NAN: Daliban Kagara: Ba zan biya N500m da suke nema kudin fansa ba, gwamna Niger ya jaddada
Wannan jawabi ya biyo bayan zaman da babban Malamin addini, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, yayi yan bindiga a dajin Tagina, garin dake iyakan jihar Neja da Birnin Gwari a Kaduna.
A jawabin hadimin Malamin, Salisu Hassan Webmaster, ya saki kuma Legit ta samu, ya yi nasiha ga yan bindigan kan muhimmancin sulhu.
Sheikh Gumi ya gana da shugaban yan bindigan, Dogo Gide.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng