Mutane a jihar Borno sun gudu daga muhallansu yayinda Soji suke artabu da Boko Haram

Mutane a jihar Borno sun gudu daga muhallansu yayinda Soji suke artabu da Boko Haram

Daruruwan mutane sun gudu daga muhallansu yayinda wasu yan ta'addan Boko Haram suka kai hari wani gari a jihar Borno ranar Juma'a.

Yan ta'addan sun dira garin Dikwa ne misalin karfe 6:05 na dare, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi amma Sojoji suka shiga artabu da su.

Sai da aka kwashe awanni ana musayar wuta.

"Sun shigo Dikwa misalin karfe 6:05 na yamma, sun harbi ko ina," wani mai idon shaida ya bayyanawa Daily Trust.

"Harin ya zo wa soji da bazata. Dubunnan mutanenmu na daukar mafaka yanzu a cikin daji."

Wannan hari ya biyo bayan harin da yan ta'addan suka kai Marte, inda suka kori Soji daga barikinsu.

DUBA NAN: Sheikh Gumi ya rokawa 'yan bindiga gafara daga gwamnatin tarayya

Mutane a jihar Borno sun gudu daga muhallansu yayinda Soji suke artabu da Boko Haram
Mutane a jihar Borno sun gudu daga muhallansu yayinda Soji suke artabu da Boko Haram
Source: UGC

DUBA NAN: Kuma dai! Yan bindiga sun sake kaiwa mutane hari jihar Neja

A bangare guda, a ranar Juma'a, gwamnatin jihar Gombe ta sanya kullen sa'o'i 24 sakamakon dakatar da titin Yola zuwa Gombe wanda yake hana isa karamar hukumar Billiri dake cikin jihar, saboda babbar kujerar sarauta ta Mai Tangale.

Daruruwan mata sun taru a wurare suna zargin da gangar gwamnatin Yahaya tayi hakan saboda ta zabi duk wanda ta ga dama ba wai zabin jama'a ba.

Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin kullen bayan wani kwarya-kwaryan taro da tayi da sakataren jihar, Farfesa Ibrahim Njodi, saboda hakan ne zai samar da zaman lafiya a yankin.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel