Matata ta kan sharara min mari duk lokacin da na ladabtar da yaran mu, miji ya fadawa kotu

Matata ta kan sharara min mari duk lokacin da na ladabtar da yaran mu, miji ya fadawa kotu

- Mai gida ya yi karar matarsa da suka shafe shekaru 14 a kotu yana neman a raba auren

- Mai gidan, Oyeniyi Oyedepo ya ce matarsa ta kan mare shi duk lokacin da ya ladabtar da yaransu

- A bangarenta, matar, Iyabo, ta amsa cewa ta mare shi amma saboda ya lakada mata duka ne

Wani ma'aikacin gwamnati, Oyeniyi Oyedepo, a ranar Juma'a ya shaidawa kotun gargajiya da ke Ibadan ta raba aurensa da matarsa, Iyabo, kan cewa ta kan mare shi duk lokacin da ya ladabtar da yaransu hudu.

Oyedepo, cikin karar da ya shigar ya ce matarsa na marinsa saboda yana ladabtar da yaransa, The Nation ta ruwaito.

Matata ta kan sharara min mari duk lokacin da na ladabtar da yaran mu, miji ya fadawa kotu
Matata ta kan sharara min mari duk lokacin da na ladabtar da yaran mu, miji ya fadawa kotu. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan ɗalibar da ta tafi makaranta da bindiga za ta harbi malamin da ya ce ta aske gashinta mai launi

"Iyabo ta lalata aurenmu. Ta kan nuna wa yaran mu kauya fiye da ni.

"Duk lokacin da na ladabtar da daya daga cikin yaran mu idan sun yi ba dai-dai ba, Iyabo ta kan fusata kuma ta mare ni.

"Ba ta min biyayya ga shi ba ta da karamci," in ji Oyedepo.

Iyabo, yar kasuwa, ta amince da raba auren.

"Miji na bai da natsuwa kuma kazami ne. Baya tsaftace dabobin da ya ke kiwo a gidan mu.

"Eh, na mare shi. Amma saboda ya min duka ne kuma ya ce in bar masa gidansa.

"Bugu da kari, ya cika neman mata, son da na ke masa ya gushe a rai na," in ji Iyabo.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Ƴan Nigeria ba su buƙatar izini kafin su zauna a dazukan Ondo

Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade, ya ce akwai yiwuwar yin sulhu idan har suna son cigaba da zaman auren idan za su iya yi hakuri.

Odunade ya gayyaci yan uwan Oyedepo da Iyabo su zo su shiga tsakani.

Ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Afrilu.

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Wasanni da Matasa a Nigeria, Hon. Solomon Dalung ya ce an saka gurbataciyyar siyasa a cikin batun tsaro a Nigeria har da kai ga wasu kasuwanci suke yi da rashin tsaron.

A hirar da tsohon ministan ya yi da wakilin Legit.ng Hausa a ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu game da sace-sacen yara a makarantu, Dalung ya ce akwai batun sakacin tsaro daga hukumomi sannan akwai siyasa.

A cewar Dalong akwai wadanda suka mayar da rashin tsaro kasuwanci ta yadda idan an samu lafiya ba za su ci abinci ba.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel