ICPC ta bankado badakalar kudi a Ma’aikatun Gwamnati a kasafin kudin 2017, 2018, 2019

ICPC ta bankado badakalar kudi a Ma’aikatun Gwamnati a kasafin kudin 2017, 2018, 2019

- ICPC ta gano irin barnar da wasu Ma’aikatun Gwamnati suka rika tafkawa

- Hukumar ta ce MDAs su kan karkatar da kudi daga cikin kasafin kudinsu

- Ana yin awon gaba da kudin ne musamman a ma’aikatun lafiya da na ilmi

Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da makamantan laifuffuka a Najeriya, ta zargi wasu ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyi (MDA) da rashin gaskiya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa wadannan ma’aikatun gwamnati su na taba kasafin kudin kasar.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya bayyana wannan a lokacin da ya zauna da manema labarai a ranar Laraba, 17 ga watan Fubrairu, 2021, a Abuja.

Bolaji Owasanoye ya ke cewa facaka da dukiyar al’umma daga kasafin kudi da wadannan ma’aikatu su ke yi ya jefa tattalin arzikin Najeriya a matsala.

KU KARANTA: Shiru ka ke ji game da binciken da Buhari ya sa aka yi a EFCC - Lauyan Magu

Owasanoye ya ce ICPC ta shigo da wani tsari da ake kira SSR wanda ya nuna yadda MDA a karkashin ma’aikatun ilmi da lafiya su ke ta wawurar kudi.

“Bincikenmu ya nuna mana cewa mafi yawan MDAs su na taba kasafin kudinsu, wanda hakan ya sa ake ba ma’aikata kudin da ya zarce bukatarsu.” Inji Owasanoye.

"A 2019, ICPC ta yi bincike a kan ma’aikatu 208, ta gano cewa an cinye rarar Naira biliyan 31.8 da aka samu na hidimar ma’aikata daga shekarun 2017 da 2018."

Wadannan ma’aikatu sun karkatar da Naira biliyan 19.8 da 9.2 da aka ware domin albashi da ayyuka.

KU KARANTA: Aisha Buhari @ 50; Gwamna Sanwo-Olu ya yabi Mai dakin Shugaba Buhari

ICPC ta bankado badakalar kudi a Ma’aikatun Gwamnati a kasafin kudin 2017, 2018, 2019
Bolaji Owasanoye da Buhari Hoto:www.channelstv.com
Asali: UGC

Har ila yau, ICPC ta hana ma’aikatu wawurar Naira biliyan 42 wadanda su ka yi kwantai a 2019, ta maimaita irin wannan kokari a kan wasu Naira biliyan 147 a 2020.

Owosanoye ya ce binciken na su ya nuna an yi gaba da kudin da aka ware domin ciyar da yaran makaranta a lokacin da gwamnati ta sa dokar kulle a shekarar 2020.

A bara kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirin rushe hukumar yaki da cin hanci da rashawa watau ICPC da kuma takwararta, EFCC.

Za a hada hukumomin biyu inda ake sa ran cewa sabuwar hukumar da za a kafa, za ta tabbatar 'yan kasa sun amfana da kudin da aka karbo daga hannun barayi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng