'Yan bindiga: Kungiyoyin Yarbawa da Ibo da Tsakiya sun yi wa Gumi kaca-kaca
- Shugabannin kungiyoyin yankunan Yarbawa, Ibo, da jihohin tsakiya sun caccaki Sheikh Gumi kan neman yi wa yan bindiga afuwa
- Kungiyoyin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanin su sun ce yanzu anyi walkiya sun gane manufarsa
- Shugabannin yankunan Yarbawa, Ibo da jihohin tsakiyar sun ce ba dai-dai bane Gumi ya rika kwatanta yan bindiga da tsagerun Niger Delta
Shugabannin kungiyoyin kudu da yankunan jihohin tsakiya, a ranar Alhamis sun cacaka Sheikh Ahmad Gumi kan cewa yan bindiga suna fada ne saboda rashin adalcin da Nigeria ta yi wa arewa, Vanguard ta ruwaito.
A cikin wani sanarwa ta suka fitar mai taken 'Gumi ya yaye gyalen', kungiyar ta tambayi Gumi kacewa shin ko Hausawa na zanga-zanga kan rashin adalcin da Fulani ke musu da sauran yan Nigeria'.
DUBA WANNAN: Hukumar asibiti ta sallami sarauniyar kyau daga aiki saboda tsabar 'kyanta'
Sanarwar na dauke da sa hannun Yinka Odumakin (Kudu maso Yamma), Cif Guy Ikokwu (Kudu maso Gabas), Sanata Bassey Henshaw (Kudu maso Kudu) da Dr. Isuwa Dogo (Middle Belt).
Wani sashi na sanarwar ya ce: "Kungiyar shugabannin kudu da jihohin tsakiya ba ta yi mamakin yadda Sheikh Gummi ya nuna kansa a AIT da safen yau, inda ya ke neman a yi wa yan bindigan da ya ce arewa suka nema wa hakkinta afuwa.
"Daga cikin rashin adalcin tabbas akwai zaben Buhari a matsayin shugaban kasa sau biyu duk da cewa kasar nan na bukatar shugaba mai lura da kula da abinda ke faruwa.
"Kusan tsawon shekaru shida kasar na cigaba da tsindumawa cikin matsaloli da suka hada da son kai da mulkar kasar kamar Jamhuriyar Fulani.
KU KARANTA: Siyan bindiga sauƙi gare shi kamar siyan burodi, in ji tubabben Ɗan Bindiga, Daudawa
"Daga cikin rashin adalcin da ake yi wa Arewa akwai kashe mutane da makiyaya ke yi a sassan Nigeria a yayin da gwamnati ke kare su tare da rangwanta musu da nuna son kai a fili da shugaban kasa ke yi."
Kungiyoyin, cikin sanarwar ta cigaba da yi wa Sheikh Gummi shagube na nuna cewa Arewa ne ke amfana da albarkatun kasa da kudanci ke samarwa tare da cewa Gummi na nema wa Fulani afuwa.
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng