Labari mai zafi: Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana da babbar murya a kan satar Dalibai

Labari mai zafi: Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana da babbar murya a kan satar Dalibai

- Majalisar dinkin Duniya ta yi tir da sace ‘Yan makaranta da aka yi a Jihar Neja

- Antonio Guterres ya fitar da jawabi na musamman ta bakin Stéphane Dujarric

- UNICEF ma ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya cewa ayi maza a kubuto da yaran

Miyagu sun shiga GSS Kagara, sun yi gaba da dalibai da ma’aikata. A karo na hudu kenan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda su na dauke yara a makaranta.

A ranar Alhamis, 18 ga watan Fubrairu, 2021, Majalisar dinkin Duniya ta yi tir da wannan lamari, ta ce bai dace irin wadannan abubuwan su na faru wa ba.

Shugaban majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres ya fitar da jawabi ne ta bakin Stéphane Dujarric.

Mai magana da yawun bakin shugaban majalisar ta Duniya, Stéphane Dujarric, ya bayyana abin da ya auku da ‘abin da ba za a yarda da shi ba kuma abin tir.’

KU KARANTA: Yadda aka sace dalibai da malaman GSSS Kagara

Antonio Guterres ya soki yadda ake kai wa wuraren karatu hari a Najeriya, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi da gaske domin ceto mutanen da aka sace.

Bayan kubuto da duka wadanda aka yi garkuwa da su, Antonio Guterres, ya bukaci gwamnati ta hukunta duk wani wanda aka samu da hannu a wannan ta'adi.

Mista Guterres ya ce ba a tabbatar da adadin wadanda aka tsere da su ba, amma ya bukaci hukumomin kasar su tabbatar da cewa an bi kadin lamarin tsaf.

Haka zalika kungiyar UNICEF ta fitar da jawabi da kalmomi masu tsauri, ta soki wannan danyen aiki.

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya zauna da Jagoran 'yan bindiga a dajin Tagina

Labari mai zafi: Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana da babbar murya a kan satar Dalibai
Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres Hoto: UN Secretary General
Source: Facebook

Rahotanni daga shafin UN sun ce UNICEF ta bakin Peter Hawkins ta bukaci a fito da wadannan yara, a maida su ga iyalinsu, ba tare da wani karinn bata lokaci ba.

Mun fara samun kishin-kishin cewa Dakarun sojojin saman Najeriya sun fara lalubo wurin da ‘Yan bindiga su ka boye yara da ma'aikatan da aka sace a garin Kagara.

Jami'an gwamnatocin Neja da Zamfara sun zauna da ‘Yan bindiga a kan mutanen da aka sace.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, wata majiya ta shaida mata jami’an gwamnatin Neja da Zamfara, sun gana da wasu ‘yan bindiga a dajin Kotonkoro, Dutsin Magaji.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel