GSS Kagara: Dakarun Sojoji sun fara lalubo wurin da ‘Yan bindiga su ka boye Yara da Ma'aikata

GSS Kagara: Dakarun Sojoji sun fara lalubo wurin da ‘Yan bindiga su ka boye Yara da Ma'aikata

- Akwai yiwuwar Sojojin sama sun gane inda aka boye Daliban da aka sace a Neja

- Haka zalika ana bincike a kan fasinjoji 18 da aka sace a garin Yakila, a jihar Neja

- Zamfara da Neja su na kokarin zama da ‘Yan bindigan da su ka yi wannan ta’adi

A ranar Alhamis, gwamnatin Neja ta kara kokari wajen ganin ta ceto dalibai da ma’aikatan da aka sace daga makarantar gwamnati da ke garin Kagara.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, wata majiya ta shaida mata jami’an gwamnatin Neja da Zamfara, sun gana da wasu ‘yan bindiga a Dutsin Magaji.

An yi wannan zama ne a wannan wuri da ke cikin jejin Kotonkoro a karamar hukumar Rafi, Neja,

“Kwamiti daga jihar Neja (tare da wasu jam’ai daga Zamfara) sun shiga jejin Kotonkoro da yammacin nan, inda ake zargin ‘yan bindigan sun kai mutanen."

KU KARANTA: Harin Neja: Ba zan biya kudin fansa ba - Gwama Bello

Majiyar ta ce wannan jeji ya yi iyaka da jihohi hudu: Kebbi, Zamfara, Neja da Kaduna, inda a nan ne ‘yan bindigan yankin su kan zauna idan wani abin ya tashi.

Jami’an gwamnatin jihar Zamfara da Neja ba su iya tabbatar da wadannan rahotanni a jiya ba,

Amma shakka-babu, Sheikh Ahmad Gumi ya gana da wasu daga cikin ‘yan bindigan da ke tsakanin Tegina da Birnin Gwaji domin a ceto wadannan Bayin Allah.

Punch ta kuma ce ta fahimci cewa jami’an tsaron da aka tura Neja daga birnin tarayya sun gano inda mutanen da aka sace su ke bayan an yi amfani da jiragen sama.

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya zauna da shugaban 'yan bindigan dajin Tagina

GSS Kagara: Dakarun Sojoji sun fara lalubo wurin da ‘Yan bindiga su ka boye Yara da Ma'aikata
Gwamna Abubakar Sani Bello Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Haka zalika sojojin sun lalubo inda aka tsare fasinjoji 18 da aka yi garkuwa da su a garin Yakila. Ana kyautatata zaton duka mutanen da aka sace su na jejin Kotonkoro.

Wani jami’in tsaro da ya yi magana da ‘yan jarida a boye a jiya, ya ce tabbas sun gano cewa sahun mutane biyun da aka sace su na wannan jeji, ta kan iyakar jihar Zamfara.

Tun a jiya kun ji cewa 'Yan sanda a jihar Neja sun fara sintiri ta sama domin gano inda dalibai da ma'aikatan makarantar kimiyyar Kagara da aka sace a ranar Laraba su ke.

Wannan ne karo na hudu da aka shiga makarantar sakandare aka sace yara a yankin Arewacin Najeriya. Hakan ya auku a Chibok, Dapchi, Kankara sai kuma GSS Kagara.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel