Rashin tsaro: Malami a Jami’ar Abuja ya ce kaf Arewa babu inda ake zaune lafiya lau a yau
- Farfesa Taufiq Abdulaziz ya yi fashin-baki a kan satar daliban makarantar da ake yi
- Malamin Jami’ar ya ce a halin yanzu babu wani yankin Arewa da ya ke zaune kalau
- Abdulaziz ya na ganin akwai hannun jami’an tsaro da wasu wajen wannan aika-aika
Farfesa Taufiq Abdulaziz, wani babban malami a jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, ya yi magana da Legit.ng Hausa game da satar yaran makaranta da ake yi.
Legit.ng Hausa ta yi magana da masanin ne bayan ‘yan bindiga sun shiga wata makarantar kwana ta gwamnati da ke garin Kagara, jihar Neja, sun sace mutane.
Farfesan ya duba lamarin ta fuskoki uku, daga ciki ya ce abin da ya faru babban kalubale ne a kan hafsoshin sojin da shugaban kasa ya nada a ‘yan kwanakin nan.
Taufiq Abdulaziz yake cewa: “Za a jarrabasu (hafsoshin sojojin), ko a duba iyakar kokarinsu, a ga ko shin za su iya kubuto yaran nan, har abin ya kawo karshe kaf.”
KU KARANTA: Shehu Sani ya soki sakacin gwamnan Neja a kan satar 'Yan makaranta
“Na uku shi ne ta fuskar tattalin arziki, garkuwa da mutane kasuwanci ne, masu sace jama’a, su na yin wannan danyen aiki ne wani lokaci da hadin-kan jami’an tsaro.”
A cewar masanin, jami’an saro su na samun kudi da halin da ake ciki, don haka abin ya ki cinye wa.
Masanin ya bayyana cewa a karshe ya kamata gwamnati ta zama ta na daukar matakin gaggawa da kar-ta-kwana a dalilin danyen aikin masu wannan ta’adin.
Farfesa Abdulaziz ya ce ana fama da garkuwa da mutane har a kudancin Najeriya, akasin abin da ake tunani na cewa ba a fuskantar wannan kalubale a wajen Arewa.
KU KARANTA: Rashin kwarewar jami'an tsaro ya jawo ake sace dalibai - Dalung
Amma Farfesan ya yarda cewa babu inda ake cikin kwanciyar hankali a kasar Arewa. Ya ce: “Babu inda ake zaman lafiya a Arewa, wannan ce gaskiyar magana.”
“Saboda a Arewa akwai wasu wuraren da doka ba ta aiki, abin takaici ne.” Malamin jami’ar ya ce wasu su ka kirkiro wannan a lokacin da ake kiran mulki ya bar Arewa.
Da ake magana da Farfesa Taufiq Abdulaziz, kun ji ya bayyana cewa lamarin siyasa na daya daga cikin mamyan abubuwan da ke ta’azzara matsalar ta’addanci a kasar.
Farfesan yake cewa a duk lokacin da ake shirin mika mulki, a kan yi amfani da matsalar tsaro da tattalin arziki musamman ta bangaren masu adawa, domin cin ma buri.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng