Da duminsa: Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar da su Buratai matsayin Jakadu

Da duminsa: Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar da su Buratai matsayin Jakadu

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata ya bukaci majalisar dattawan tarayya ta tabbatar da tsaffin hafsoshin tsaron Najeriya matsayin Jakadu zuwa kasashen waje.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisa ranar Talata.

Tsaffin hafsoshin tsaron da Buhari ya zaba kuma ya bukatan a tabbatar da su sune: Janar Abayomi Olonisakin (mai ritaya), Laftanan Janar Tukur Buratai (mai ritaya), Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (rtd), Air Marshal Sadique Abubakar (Mai ritaya), da Air Vice Marshal Mohammed Usman.

Majalisar dattawa ta bayyana hakan a shafinta na Tuwita:

Da duminsa: Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar da su Buratai matsayin Jakadu
Da duminsa: Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar da su Buratai matsayin Jakadu Credit: NGRSenate
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel