'Yan Najeriya su na maidawa Ministan Buhari martani na cewa a tsaya a rika fada da 'Yan bindiga
- Ministan tsaro ya ce ya kamata mutane su tsaya idan Miyagu sun kawo hari
- Bashir Magashi ya kira ‘Yan kasar ragwaye, ya ce a zamanin da, ba su tsoro
- Jama’a sun yi kaca-kaca da Ministan a Twitter a dalilin wannan kalamansa
Mutane su na cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da bayanin da Ministan tsaro na kasa, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ya yi a jiya.
Bashir Magashi ya yi kira ga al’umma cewa kar su zama ragwaye idan ‘yan bindiga sun kawo masu hari, ya ce da su ke yara, ba su jin tsoron miyagu.
Wannan kalamai da su ka fito daga bakin Ministan tsaron sun jawo surutu. Legit.ng Hausa ta tattaro maku abin da wasu su ke fada a dandalin Twitter.
“Bai kamata Ministan tsaro ya fadi wannan magana ba. Mutanen da ba su da makami, bai kamata su fuskanci masu bindigogin AK-47 da makaman RPG ba. Ka yi aikinka, ko kuma ka yi murabus.” Inji Dr. Ogbeni Dipo.
KU KARANTA: Ko Buhari ya sallami Ministan labarai, ko ayi waje da shi daga APC
Wani ya ce: “Mu ke neman sana’ar da za mu yi, da wutar lantarkinmu, ruwanmu, da lafiyarmu, yanzu kuma Ministan tsaro ya ce mu ba kanmu kariya, shin menene amfanin gwamnatin Najeriya?
Husnah ta lura Ministan da yake kiran mutanen zamanin nan ragwaye, bai iya yawo sai da dogarai.
Dr. Olunfunmilayo kuwa ya ce: “Ministan tsaro ya fito ya na cewa ‘Yan Najeriya su kare kansu daga miyagu. Amma kuma shi din dai ba ya goyon bayan a ba jama’a bindiga. To da me za mu kare kanmu, da wukar burodi ko takalmi.”
Shi kuwa FS Yusuf da ya ji maganar Ministan, sai ya ce: “Zan fa saida koda na guda ne in bar kasar nan.”
KU KARANTA: Za mu nemo aron kudi daga kasar Brazil - Nanono
"Ministan da ke yawo da bariki guda na sojoji su na tsare shi ya na kiranmu ragwaye, saboda ‘yan ta’adda sun kawo mana hari. Mu na da Ministocin da sun raina ‘Yan Najeriya", a cewar Raymond.
Keyser Soze ta ce ya kamata Ministan ya ajiye aikinsa, ita kuwa Anita Egboibe ta ce da zarar ta ji wani mutumin-da ya fara bada labarin zamaninsu, ta san shirme kurum zai fada.
A ranar Laraba, kun ji Ministan tsaro na kasar nan, ya na cewa 'yan Najeriya su rika ba kansu kariya daga 'yan bindigan da su ke kai wa al'umma hari musamman a Arewa.
Bashir Magashi ya ba jama'a shawara ka da su nuna gazawarsu a fili, su tsaya ayi ta maza, domin kuwa 'yan bindigan su na zuwa ne harsashai kalilan da ba su kai sun kawo ba.
M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.
Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.
A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi
Asali: Legit.ng