Shugaba Buhari zai karbo sabon bashin Naira Biliyan 500 domin bunkasa harkar noma

Shugaba Buhari zai karbo sabon bashin Naira Biliyan 500 domin bunkasa harkar noma

- Gwamnatin Najeriya ta na shirin cin bashin $1.2 daga wasu bankunan ketare

- Wannan bashin kudi da za a ci zai taimaka wajen zamantar da sha’anin noma

- Ministan gona ya ce ‘yan kasuwa za su biya wannan bashi nan da shekaru 15

Gwamnatin tarayya ta shiya tsaf domin cin bashin Dala biliyan 1.2 daga wasu bankunan kasar waje da nufin inganta harkar gona a Najeriya.

Punch ta ce za a karbo aron wannan kudi ne daga bankin Dutch Bank da kuma babban bankin nan da ake kira Development Bank na kasar Brazil.

Jaridar ta ce Hadimin Ministan harkar gona, Andrew Kwasari, ya shaida wa ‘yan jarida wannan a Abuja, a ranar Laraba, 17 ga watan Fubrairu, 2021.

Mai ba Ministan gonan shawara yake cewa wannan shiri ya na cikin tsarin Green Imperative Project.

KU KARANTA: Sojoji na neman 'yan bindigan da su ka sace dalibai a Neja

Gwamnatin tarayya ta shigo da wannan tsari na Green Imperative Project ne domin inganta harkar gona, ta yadda za a rika noma da na’urorin zamani.

“Green Imperative zai zamanantar da noma, ya samar da kayan gyaran amfani. Za a kafa cibiyoyi da za su kula da wannan a duk wata karamat hukuma.”

Ya ce: "Masu hannun jari ne za su kula da wannan aiki. Saboda haka ‘yan kasuwa ne za su sa lura da duka cibiyoyin nan, su ne za su biya wannan bashi.”

Hadimin Ministan ya bayyana cewa za a biya wannan bashi mai ruwan 3% a cikin shekaru 15.

KU KARANTA: Lauyan Magu ya koka a kan yadda aka fatattaki tsohon Shugaban EFCC

Shugaba Buhari zai karbo sabon bashin Naira Biliyan 500 domin bunkasa harkar noma
Ministan harkar noma, Sabo Nanono Hoto: @Nanonosabo
Asali: Twitter

Kwasari yace gwamnatin Najeriya za ta aro fam €995m ($1.2bn). idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, wannan bashi da za a karbo zai kai Naira biliyan 500.

A tsakiyar makon nan ne ku ka ji cewa fitaccen mai kudin Afrikan nan, Aliko Dangote ya narka abin da ya kai akalla Naira Biliyan 10 a harkar ilmi a Najeriya.

A cikin 'yan kasuwa masu zaman kansu, Dangote bai da sa’a a kokarin farfado da ilmi domin yara fiye da 1, 000 ya dauka, ya horar a makarantar Dangote Academy.

Attajirin ya kashe wa irinsu ABU, BUK, da sauran Jami’o’i a Enugu da Kano makudan kudi.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel