Da duminsa: Mun bazama neman yan bindigan da suka sace daliban Kagara, Hukumar Soji

Da duminsa: Mun bazama neman yan bindigan da suka sace daliban Kagara, Hukumar Soji

- Hukumar Soji ta saki jawabinta na farko kan sace dalibai makarantar sakandare a Kagara

- Wannan ya biyo bayan jawabin Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi

- Gwamnan Neja ya tabbatar da sace dalibai akalla 27 da Malamai 3

Hukumar Sojin Najeriya ta ce ta tura jami'anta neman masu garkuwa da mutanen da suka yi awon gaba da daliban makarantar sakandare GSC Kagara, jihar Neja.

Diraktan hulda da jama'a na hukumar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba a Abuja.

Yerima ya ce hukumar ta bazama neman yan bindigan domin ceton yaran.

Ya ce rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun samu shiga cikin makarantan ne da safiyar Laraba suka sace daliban makaranta da malamansu.

"Hukumar Sojin Najeriya bisa aikinta na tabbatarwa daukacin yan Najeriya cewa jami'anta tare da wasu jami'an tsaro na kan neman tsagerun da kuma ceto yaran da aka sace," yace.

"Bayan haka, hukumar Sojin na kira ga jama'a su baiwa hukumomin tsaro kowani labarin da suka samu kan tsagerun."

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da cewa an sace dalibai 27, ma'aikata 3, da wasu mutane 12 a cikin makarantan.

DUBA NAN: Ya kamata a kafa doka kan man canza launin fata (Bilicin), Tinubu

Da duminsa: Mun bazama neman yan bindigan da suka sace daliban Kagara, Hukumar Soji
Da duminsa: Mun bazama neman yan bindigan da suka sace daliban Kagara, Hukumar Soji Credit: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

KU KARANTA: Farashin litan man fetur zai iya tashi N190 yayinda farashin danyen mai ya kai $63

A wani labarin kuwa, Shugaba Muhammadu Buhari yayi Allah-wadai da sace dalibai da ma'aikatan makarantar GSSS dake Kagara, jihar Neja a ranar Talata 16 ga watan Fabrairu.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ne ya wallafa jawaban shugaban kasan a shafinsa na Facebook yau Laraba da misalin karfe 11:44 na safe.

A cewar shugaban, ya samu labarin faruwar lamarin kai harin 'yan ta'adda da ya auku cikin dare, wanda har ya zuwa yanzu ba a gano adadin ma'aikata da daliban da aka sace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel