Ba mu da niyyar kara farashin man fetur yanzu, Kamfanin NNPC

Ba mu da niyyar kara farashin man fetur yanzu, Kamfanin NNPC

- Farashin dan mai a kasuwar duniya ya tashi zuwa $63 kan kowace ganga

- Hakan ya sa ana tsoron farashin man fetur a gidajen man Najeriya

- Ministan Mai ya ce yan Najeriya su shirya jure tsadar mai

Babu shirin kara farashin litan man fetur, kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ya bayyana ranar Talata.

Janar Manaja na sashen yada labaran NNPC, Dr Kennie Obateru, ya yi watsi da jita-jitan dake ana shirin kara farashin litan man fetur.

The Nation ta ruwaito shi da cewa: "NNPC bata kara farashin mai a Depot ba. Ina da tabbacin NNPC ba ta da niyyar kara farashin a Febrairu."

A cewarsa, NNPC na da isasshen mai a jiye da zai ishemu na tsawon kwanaki 40. Ya kwantar da hankalin jama'a su daina tsoron cewa akwai yiwuwar karancin mai.

Obateru ya yi kira ga hukumar DPR ta damke yan kasuwan mai dake boye man fetur.

"Muna da isasshen mai da zai ishemu na tsawon kwanaki 40. Idan mutane na boye mai ko kara farashin, aikin DPR ne ta dauki mataki," yace.

KU KARANTA: Ya kamata a kafa doka kan man canza launin fata (Bilicin), Tinubu

Ba mu da niyyar kara farashin man fetur yanzu, Kamfanin NNPC
Ba mu da niyyar kara farashin man fetur yanzu, Kamfanin NNPC Credit: NNPC
Asali: UGC

DUBA NAN: An kafa kwamiti na musamman don binciken jami'in Hisban da aka kama da matar aure

Kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu (IPMAN) ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta koma biyan tallafin mai saboda farashin da tataccen mai ke isowa Najeriya ya kai N180 ga lita.

Mataimakin shugaban IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandi, ya bayyana cewa gwamnati ta zabi daya, cire tallafin gaba daya ko kuma biya gaba daya.

A yanzu, gidajen mai a Najeriya basu kara farashin mai ba.

A binciken da Legit ta gudanar a gidajen mai a birnin tarayya Abuja, gidajen mai na sayar da litan mai har yanzu tsakanin N159 da N162.

A yanzu dai ana sayar da litan man fetur ne tsakanin N159 da N165 a gidajen mai a fadin tarayya, amma wannan farashin zai iya haurawa N190 a kwanakin nan yayinda farashin da mai ke shigowa Najeriya yau N180 daga N151 sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Tashin farashin danyen mai daga $58 zuwa $63 a jiya na nufin cewa kudin masu tace danyen mai zai karu wajen saya, tafiyarwa da kai mai ga kwastamomi.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel