'Yan bindiga sun tsere bayan arangama da sojoji a Katsina
- Sojojin Nigeria sun dakile wani hari da wasu yan bindiga suka kai wasu kauyuka a Katsina
- Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigan sun kai hari garin Tashar Bawa misalin karfe 10.15 na safiyar ranar Litinin
- Yan bindigan sun yi gaba zuwa kauyen Sayau Dangado a nan ne sojoji suka iso suka tarwatsa su suka cece mutanen garin
Dakarun sojojin Nigeria sun fatattaki wasu yan bindiga da suka kai hari a garuruwan Tashar Bawa da Sayu Dangado a karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina a ranar Litinin, The Punch ta ruwaito.
Majiyoyi sun ce yan bindigan sun isa garin Tashar Bawa misalin karfe 10.15 na safe sannan suka sace babura da wasu kayayyaki da suka hada da wayoyin salula.
KU KARANTA: Hotunan ganawar Buhari, Zulum, Buni da dattawan Borno da Yobe a Aso Rock
DUBA WANNAN: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano
Daga nan sun kuma kara gaba zuwa Sayau Dangado inda suke shirin sace wasu mazauna garin a yayin da dakarun sojojin suka isa kauyen.
An ruwaito cewa ga ganin sojojin, yan bindigan sun yi watsi da wasu kayayyakin da suka sace suka tsere.
An yi kokarin tabbatar da afkuwar lamarin daga 17 Brigade ta Nigerian Army amma hakan bai yi wu ba domin sun ce a tuntubi Hedkwatar Tsaro da ke Abuja.
Kazalika, yunkurin da aka yi na ji daga bakin Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah domin jin ta bakinsa shima ya ci tura.
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng