UCL: Mbappe ya sa Barcelona ta ji wuju-wuju, ya zura kwallaye 3 yayin da aka tashi 4-1

UCL: Mbappe ya sa Barcelona ta ji wuju-wuju, ya zura kwallaye 3 yayin da aka tashi 4-1

- Kylian Mbappe ya cinye taro a wasan Barcelona da kungiyar Paris Saint-Germain

- Moise Kean da Mbappe sun taimakawa Paris Saint-Germain ta yi nasara da ci 4-1

- Rashin Neymar da Di Maria bai hana Barcelona shan kashi a gasar kofin Turan ba

Kylian Mbappe ya ba kungiyar Paris Saint-Germain gagarumar nasara yayin da ya jefa kwallaye uku a raga a wasansu da Barcelona a ranar Talata.

ESPC ta ce tauraron ya yi amfani da damarsa yayin da Neymar Jr. da Angel Di Maria ba su samu damar hadu wa da Barcelona a gasar kofin Nahiyar Turai ba.

Lionel Messi ya bude taron na jiya inda ya ci bugun finariti a minti na 26. Kafin a kai ko ina, ‘dan wasa Kylian Mbappe, ya maida martani a minti na 33.

KU KARANTA: 'Yan wasan Barcelona sun kamu da COVID-19

A minti na 65 Mbappe wanda ya yi shekaru biyu bai ci kwallo a wannan gasa a wannan mataki ba, ya ba PSG nasara. Daga baya Moise Kean ya ci kwallo ta uku.

Bayan ‘yan mintuna, mai tsaron ragar Barcelona Marc-Andre ter Stegen, ya yi kokari ya hana ‘dan wasan gaban PSG, Kylian Mbappe, sake zura wani kwallon a raga.

Duk da haka, a minti na 85, Mbappe ya kammala aikinsa, ya ci kwallo na uku. Hakan ya ba Mauricio Pochettino wanda ya karbi ragamar PSG kwanaki nasara.

Barcelona ta fara wasan ne da farin cikin cewa ‘dan wasan baya, Gerard Pique ya warke, ya dawo kwallo.

KU KARANTA: Ronaldo ya ci kowa kwallaye a Duniya

UCL: Mbappe ya sa Barcelona ta ji wuju-wuju, ya zura kwallaye 3 yayin da aka tashi 4-1
Mbappe da Messi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ben Hayward, masanin harkar kwallon kafa, ya bayyana cewa ‘yan wasan Barcelona sun dade su na shan wahala idan su ka kara da kungiyoyin da su ke da gudu sosai.

Kocin PSG, Mauricio Pochettino ya bada labarin yadda Mbappe ya yi masa alkawarin doke Barcelona, wanda kafin yanzu sau daya kocin ya taba yin galaba a kan ta.

A watan da ya gabata ne Kungiyar Bilbao ta yi waje da Madrid, sannan ta doke Barcelona, ta dauki kofin Super Cup wanda Ronald Koeman ya sa ran cewa zai karya da shi.

A wannan wasa Tauraro Lionel Messi wanda ya buga wa kungiyar Barcelona wasanni har 750 ba tare da jan kati ba, ya karya tarihin da ya kafa, aka ba shi jan kati a wasan.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel