Yanzu-yanzu: Ƴan Boko Haram sun ƙona gidaje fiye da 140 a ƙauyukan Borno, sun sace dabobi da kayan abinci
- Yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka uku a karamar hukumar Biu da ke kudancin jihar Borno
- Garuruwan da yan ta'addan suka kai wa harin sun hada da Egiri, Zira I da Zira II inda suka kone gidaje, suka sace kaya
- Majiyoyi sun ce wannan shine karo na biyu da yan ta'addan ke kai hari a kauyen da ke karamar hukumar Biu
Wasu da ake zargi mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun kai hari wasu kauyuka a karamar hukumar Biu jihar Borno inda suka kone gidaje a kalla guda 140.
Bayan kone gidajen yan ta'addan sun kuma sace kayayyakin abinci da dabobi kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Asali: Twitter
Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Egiri, Zira I da Zira II.
Zira na da nisan kilomita 5 daga kauyen Gur da aka kai hari a ranar Juma'a da ta gabata inda mutum hudu suka riga mu gidan gaskiya sannan aka kone gidaje da ababen hawa.
KU KARANTA: An fara bincikar jami'in Hisbah da aka kama da matar aure a ɗakin Otel a Kano
Zira da Gur garuruwa ne da ke kusa da Buratai, garin su tsohon babban hafsan sojojin kasan Nigeria, Janar Yusuf Tukur Buratai.
A cewar majiyoyi, wannan shine karo na biyu da yan ta'addan ke kai hari kauyen a cikin wata guda.
Wata majiya daga karamar hukumar Biu ta tabbatar wa TVC News barnar da yan ta'ddan suka yi a garuruwan guda uku.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun tsere bayan arangama da sojoji a Katsina
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun, daga karshe ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Omisore, a ranar Litinin, 15 ga watan Fabarairu ya ziyarci mazabarsa ta 6, Moore, a Ile-Ife, a tare da tawagar mataimakin gwamna, Benedict Alabi, domin ya karbi katinsa na APC.
Omisore ya yi takarar kujerar gwamna a shekarar 2018 a karkashin inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP).
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng