Shugaban kasa Buhari ya yi wa Jami’an ‘Yan Sanda na’am da yi wa Miyagun Fulani tonon silili

Shugaban kasa Buhari ya yi wa Jami’an ‘Yan Sanda na’am da yi wa Miyagun Fulani tonon silili

- Shugaba Muhammadu Buhari ya nesanta kansa daga aika-aikar wasu Makiyaya

- Shugaban kasar ya ce ba ya goyon bayan garkuwa da mutane da barnar da ake yi

- Buhari ya ba ‘Yan Sanda umarnin bayyana duk Fulanin da ake shari’a da su a kotu

A ranar Litinin, 15 ga watan Fubrairu, 2021, fadar shugaban kasa ta bukaci ‘yan sandan Najeriya su fito da sunayen duk Fulanin da ake zargi da laifi.

Fadar shugaban kasa ta umarci jami’an ‘yan sanda su wallafa sunayen gaba daya makiyaya Fulani da ake shari’a da su a kotu da zargin aikata laifuffuka.

Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da rahoto, shugaban kasar ya bada wannan umarni ne domin nuna babu hannunsa a wajen wanke makiyaya Fulani.

Ana zargin mai girma Muhammadu Buhari da yi wa ta’adin Fulani rufa-rufa saboda kabilarsu daya.

KU KARANTA: Hausawa fiye da 3000 sunn fake a gidan Sarkin Shasha

Mai ba shugaban kasar shawara wajen yada labarai, Garba Shehu ya bayyana wannan a lokacin da aka yi hira da shi a shirin ‘Sunrise Daily’ na Channels TV.

Ya ce: “Shugaban kasar ya damu iya damu wa a kan halin da ake ciki, ya na sane cewa nauyin gwamnati ne ta yi aiki da mutane, su tsare rayukan al’umma.”

“Kuma su kawo karshen rikicin da ake yi, daga garkuwa da mutane zuwa sababbin laifuffukan da ake yi na fadan kabilanci. Ba ya tare da su, ba ya goyon baya.”

“Ina fatan hedikwatar ‘yan sanda za ta dauki nauyi, ta wallafa cikakken sunayen duk makiyaya Fulani wadanda ake shari’a da su a jihohi, musamman Benuwai.”

KU KARANTA: Dole Buhari ya yi maganin hare-haren da ake kai wa Fulani – Matawalle

Shugaban kasa Buhari ya yi wa Jami’an ‘Yan Sanda na’am da yi wa Miyagun Fulani tonon silili
Shugaban kasa Muhammadu Buhari Hoto: @MBuhari
Source: Twitter

“Ana shari’a a kotu, an gurfanar da wasu, an same su da laifi, kuma babu yadda za ayi shugaban kasa ya tsoma baki. (Buhari) ba zai yi abin da su ke fada ba.” Inji Shehu.

Dazu kun ji cewa tawagar Gwamnonin Arewa ta isa Kaduna da nufin yin zama kan rikicin Shasha. Ofishin NSA ne ya hada wannan taro a madadin shugaban kasa.

Fadar Shugaban kasar ta kira taron ne domin a kawo karshen kashe-kashen da ake yi. Gwamnoni sun zauna da nufin magance kashe-kashen da ake yi wa mutane a Kudu.

Malam Nasir El-Rufai ya ce ana yin wannan zama ne a gidan Arewa House da ke Kaduna.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel