Shugaba Buhari ya yi na’am da dakatar da Magu, ya nada Umar – Inji Malami
Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin Najeriya, Abubakar Malami, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu daga EFCC.
Abubakar Malami SAN ya ce Ibrahim Magu ya bar kujerar da ya ke kai na mukaddashin shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa.
Malami ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya fitar a ranar Juma’a, 10 ga watan Yuli, ta bakin mai magana da yawun bakinsa, Dr. Umar Gwandu.
Ministan tarayyar ya kuma bada sanarwar cewa an nada darektan gudanarwa na EFCC, Mohammed Umar a matsayin mukaddashin shugaban hukumar.
Kamar dai yadda aka rika samun rade-radi, Mohammed Umar ne zai rike hukumar EFCC na rikon kwarya kafin lokacin da za a bayyana makomar Ibrahim Magu wanda ake bincike.
Jawabin da ministan ya fitar ya na cewa:
KU KARANTA: Lauyan da ke kare Ibrahim Magu ya bayyana halin da ake ciki
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Ibrahim Magu daga matsayin mukaddashin shugaban hukumar EFCC cikin gaggawa domin bada dama ga kwamitin shugaban ya yi cikakken bincike a karkashin dokokin kasa.”
Bayan haka, Gwandu ya kara da cewa:
“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma amince da cewa darektan harkokin gudanarwa na hukumar EFCC, Mohammed Umar, ya jagoranci aikin hukumar, har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake yi, sannan kuma a dauki mataki game da lamarin.”
An shafe kusan kwana biyar kenan ana yi wa Ibrahim Magu tambayoyi a fadar shugaban kasa. A ranar Alhamis, wasu manyan jami’o’in EFCC sun bayyana gaban kwamitin na musamman.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng