Siyasar Kano: PDP ta nemi ‘Yan Sanda su damke Shugaban APC, Abdullahi Abbas

Siyasar Kano: PDP ta nemi ‘Yan Sanda su damke Shugaban APC, Abdullahi Abbas

- PDP ta ce ta rubutawa ‘Yan Sanda takarda a kan Shugaban Jam’iyyar APC na Kano

- Abdullahi Abbas ya fito ya na wasu irin jawabai da PDP ta ce kalaman kiyayya ne

- Shehu Wada Sagagi ya ce sun rubuta takarda zuwa ga IGP domin taka masa burki

Jam’iyyar PDP ta rubuta takarda zuwa ga Shugaban ‘yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ta na neman a kama shugaban APC na jihar Kano.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jam’iyyar PDP mai adawa ta nemi a cafke Alhaji Abdullahi Abbas ne saboda zarginsa da ake yi da furta kalaman kiyayya.

Alhaji Abdullahi Abbas ya yi wani jawabi, inda aka ji ya na kiran a lallasa wanda aka kama ya je zai saci akwatin zabe a 2023, wannan ya sa PDP ta kai kara.

“Ku kai hari ku hukunta duk wanda ku ka samu zai saci kuri’a a lokacin zaben 2023. Ku dauki doka da mataki mai tsauri a hannunku, babu abin da zai faru.”

KU KARANTA: Ministan Buhari ya koka da rajistar APC da ake yi

Ya cigaba da cewa: “Na ba ku umarni ku hukunta duk wanda aka samu gaban akwatin zabe ya na shirin murdiya, wannan ukuba ta ce, babu abin da zai faru.”

“Ina kira ga matasan jam’iyyarmu, su ajiye makamansu, akwai lokacin da za su yi amfani sosai.” Inji Abbas lokacin rantsar da shugabannin kananan hukumomi.

Shugaban PDP na Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya ce sun rubuta takarda, sun aika wa shugaban ‘yan sanda na kasa da wasu hukumomin gwamnati a Najeriya.

“Ba mu yi mamaki ba, domin ya zama a jininsa, ya yi irin wannan magana. Wannan kalaman kiyayya ne.” PDP ta ce ta kai kara saboda zaman lafiyar al’umma.

KU KARANTA: Sanusi II ya yi kira ga shugabanni game da kashe-kashen da ake yi

Wada Sagagi ya ce duk da abin da shugaban na APC yake fada, ba zai hana a zabi jam’iyyar PDP a 2023 ba.

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa har yanzu yana nan a jam'iyyar PDP.

Goodluck Jomathan ya bada wannan tabbacin ne a yayin da wasu ke hasashen cewa yana shirin komawa APC, har ya nemi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Dr. Jonathan ya ce PDP jam'iyya ce da ke haba-haba da kow,a, ya bada shawarar a hada-kai.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel