Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya yi magana daga Ingila kan harin da ake kai wa ‘Yan Arewa a Kudu

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya yi magana daga Ingila kan harin da ake kai wa ‘Yan Arewa a Kudu

- Tsohon Sarkin Kano ya magantu daga kasar Ingila a kan kashe-kashen da ake yi

- Muhammadu Sanusi ya ce dole shugabanni da hukuma su kare rayukan al’umma

- Sanusi II ya ce irin wadannan rigingimu ne su ke kai ga jawo yakin basasa a kasa

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi magana game da kashe-kashen da aka yi a kudancin Najeriya, ya soki lamarin, sannan ya yi kira ga hukuma.

Da yake jawabi a wani bidiyo, Sanusi II ya ce “Mu na jin maganganu da yawa a kan abubuwan da su ke faru wa a kasa. Mu na kira ga al’umma a zauna lafiya.”

Ya yi kira ga gwamnatoci cewa; “Mu na fatan shugabanni za su maida hankali a kan abubuwa da su ke faru wa na kone-kone da kashe-kashe a wasu sassa na kasa.”

“Ayi kokari a kare rayukan mutane da rayuwarsu.”

KU KARANTA: Rikicin Oyo: Gwamnonin Jihohin Arewa sun zauna da Gwamna Makinde

“A kan mutanenmu na Arewa, duk mutumin da yake Kudu, amana ce a hannunsa. Ka da a ji zafi, a dauki mataki a hannu, ayi kokari ayi addu’a.” inji Sanusi II.

Tsohon sarkin ya yi addu’ar Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya. Har ila yau ya ja-kunne da cewa irin wannan rikici ne ya kai kasashe ga zuwa yakokin basasa.

“Irin wadannan abubuwa su ka kai ga yakin basasa a shekarar 1967, haka aka yi yakin Ruwanda. Duk inda aka yi yaki, da haka ake fara wa; ana zub-da-jini, ayi shiru.

Malam Sanusi II ya kara da cewa: “Wannan yaki ba zai haifa mana komai ba, illa koma-baya."

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya yi magana daga Ingila kan harin da ake kai wa ‘Yan Arewa a Kudu
Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II Hoto: www.withinnigeria.com
Source: UGC

KU KARANTA: Wasu Sarakunan Yarbawa sun hada-kai da masu garkuwa da mutane

“Zaman lafiya da siyasar tattalin arziki mai kyau da za ta fitar da jama’a daga kangi mu ke bukata.” A karshe Sanusi II ya yi kira ga masu hali su bada taimako.

“Masu hali da attajirai su taimaka wa makwabta, marayu da mutane daga abin da Allah ya ba su.”

A baya kun ji tsohon sarkin na Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan dambarwar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnati da malaman addini.

Sanusi II ya yabi gwamnatin Abdullahi Ganduje, kuma yi kira ga mutanen Kano su tsaya a kan koyarwar Shehu Danfodio, ya na mai sukar karantarwar Abduljabbar Kabara.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel