Hukumar Kwastam: Mun samu umarnin tabbatar da rage harajin shigo da motoci

Hukumar Kwastam: Mun samu umarnin tabbatar da rage harajin shigo da motoci

- Hukumar kwastan ta ce a karashe watan Fabarairu za'a fara tabbatar da ragin harajin shigo da motoci Nigeria

- Shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali, ya ce sun samu umarnin ne daga ma'aikatar kudi, kasafi, da tsare-tsare

- A cikin watan Disambar shekarar 2020 ne shugaba Buhari ya saka hannu akan dokar rage kudin

Hukumar hana fasa kwabri ta kasa (Kwastam, NCS) ta ce ta samu umurni daga ma'aikatar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa, na tabbatar da rage harajin da ake karba daga motocin da ake shigowa da su cikin kasar nan.

Hameed Ali, kwanturola Janar na hukumar Kwastam, ya shaidawa NAN a ranar Lahadi cewa za a tabbatar da bin wannan umurni a karshen watan Fabrairu.

A baya bayan nan dai Ali ya ce hukumar NCS na jiran umurni daga ma'aikatar ne kan wannan sabuwar doka ta rage harajin da ake karba daga hannun masu shigo da motoci Nigeria daga ƙasashen waje.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sa hannu kan dokar kudi ta 2020 a ranar 31 ga watan Disamba 2020, inda aka rage harajin da aka sanya wa motocin da ake shigowa da su kasar da suka hada da Tarakta da motocin daukar fasinja.

"An gabatar mana da wannan doka. Mun samu umurni daga ma'aikatar kudi a wannan makon, kuma muna shirye shiryen tabbatar da umurnin, duk da cewa sai mun samar da tsare tsare da zasu bamu damar tabbatar da bin dokar," a cewar Ali.

Hukumar Kwastam: Mun samu umarnin tabbatar da rage harajin shigo da motoci
Hukumar Kwastam: Mun samu umarnin tabbatar da rage harajin shigo da motoci @TheCable
Asali: Twitter

"Mu mun canja tsare tsaren mu don yin dai dai da wannan sabuwar doka. Kun san motocin daukar fasinja ne kawai aka rage wa haraji daga kaso 35 zuwa kaso biyar.

"Ina fatan nan ba da jimawa ba, nan da sati daya ko biyu, za a tabbatar da wannan doka. Za mu rabawa rassan mu domin tabbatar da an bi wannan dokar."

Shugaban hukumar Kwastam din, ya ce sabuwar dokar za ta taimakawa kasar wajen samun motocin daukar fasinjoji bayan rage harajin da aka sanya.

Ya yi nuni da cewa yawan kudaden harajin motoci da aka sanya ya kara yawaitar shigo da motoci ta barauniyar hanya a kasar.

Ali ya kuma bayyana cewa kididdiga ta nuna yadda ake shigo da motoci akalla 300,000 zuwa 400,000 Nigeria, inda ake fara hada tafiyar daga Jamhuriyar Benin.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Babbar kungiyar Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta ce ta gaji da cin kashi da barazanar da ake yi wa mambobinta kuma a halin yanzu tura ta kai bango.

Rahotanni na cigaba da bayyana yadda ake kara samun yawaitar kai hare-hare akan makiyaya da ke zaune ko xiyartar kudancin Nigeria.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Saleh Alhassan, ya ce makiyayan da ake kashewa daban da wadanda suke tafka barna a sassan Nigeria.

Naziru Dalha Taura Malamin makaranta ne kuma dalibi da ke sha'awar rubuce-rubuce akan dukkan al'amuran da suka shafi jiya da yau. Ya samu kusan shekaru hudu yana aiki da Legit.ng.

Ya kammala karatun digiri na farko a Jami'ar Bayero da ke Jihar Kano a bangaren ilimin kimiyyar sinadaran rayuwa da tasirinsu a jikin dan adam.

Za'a iya tuntubarsa kai tsaye a shafinsa na tuwita a @deluwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel