'Yan bindiga mutane ne masu kunya, in ji Sheikh Ahmad Gumi
- Sheikh Ahmed Gumi, fitaccen malamin musulunci mazaunin Kaduna ya shawarci gwamnatin tarayya ta yi wa yan bindiga afuwa
- Babban malamin a wata hira da aka yi da shi ya ce yan bindigan mutane ne masu kunya matuka sai ka hadu da su zaka gane
- Gumi ya ce yan bindigan suma tunda farko an sace musu shannun su ne kuma an dade ana musu kwace don haka sun cancanci afuwar
Fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin garin Kaduna Sheikh Ahmad Gumi ya ce yan bindiga mutane ne masu kunya.
A cewar malamin, an dade ana sace wa yan bindigan shanun su tare da yi musu kwace don haka ya kamata a yi musu afuwa sannan a biya su diyya.
DUBA WANNAN: Turkmenistan: Shugaban ƙasa ya naɗa ɗansa a matsayin 'mataimakinsa'
A hirar da aka yi da shi da The Punch, malamin ya bayyana yan bindigan a matsayin mutane masu kunya wadanda shanunsu kawai suka damu da su.
Ya ce gwamnatin tarayya ta musu afuwa za su ajiye ajiye makamansu.
"Wadannan mutanen (yan bindiga) sun san yadda za su hada kansu kuma sun fara kai hare-hare kauyuka. Da ka taba daya daga cikinsu, dukkan su za su taru su kai hari a kauye. A dazuka suke hada kansu. Don haka, ba abu bane mai kyau a kai musu hari, maganan gaskiya kenan," in ji Gumi.
"Hausawa suna shan wahala don haka sun dena kai wa makiyaya fulani hari. Don haka kada mu kai musu hari. Mu yi sulhu da su kawai kuma mutane ne masu kunya. Idan ka hadu da su, suna da kunya sosai.
KU KARANTA: Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan
"Idan ka musu afuwa, za su ajiye makamansu. Sai ka shiga ka gina musu makarantu, asibitoci sannan ka kidaya su; a yi musu rajista sannan ya iya juya su.
"Ba za ka iya cin nasara ta hanyar bindiga ba. Maganan gaskiya, sun fi sojojin mu sanin daji. Don haka ya fi dacewa a yi sulhu da su."
A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.
Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.
Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Asali: Legit.ng